| Hausa
WASANNI
2 MINTI KARATU
Birnin Istanbul zai karɓi baƙuncin gasar UEFA Europa ta 2026, da gasar Conference ta 2027
Kwamitin zartarwa na hukumar UEFA ya yanke cewa za a gudanar da wasannin ƙarshe na gasar Europa ta 2026 da na Conference na 2027 a filin wasa na Besiktas da ke birnin Istanbul.
Birnin Istanbul zai karɓi baƙuncin gasar UEFA Europa ta 2026, da gasar Conference ta 2027
Birnin Dublin na Ireland zai karɓi baƙuncin wasan ƙarshe na gasar Europa. / Hoto: AFP / AFP
22 Mayu 2024

Hukumar gudanarwa ƙwallon ƙafa a Turai, ya yanke cewa za a gudanar da wasan ƙarshe na gasar Europa na 2026 a filin wasa na ƙungiyar Besiktas, wato filin Tupras Stadium da ke Istanbul.

Haka nan kuma, birnin na Istanbul zai karɓi baƙuncin wasan ƙarshe na gasar Europa Conference ta 2027.

A sanarwar da mamban kwamitin gudanarwa na UEFA, Servet Yardimci ya fitar, taron na hukumar UEFA ya gudana ne a birnin Dublin babban birnin Ireland, a Laraba.

Filin wasa na Tupras Stadium, wanda a baya ake kira da Vodafone Park, shi ne ya karɓi baƙuncin gasar UEFA Super Cup ta 2019, inda aka buga wasa tsakanin Liverpool da Chelsea.