Kungiyar PSG ta dakatar da tattaunawa kan sabunta kwantiragin Lionel Messi a kulob din wata uku kafin kwantiraginsa ya kare/ Hoto: Anadolu

Kyaftin na Ajantina Lionel Messi zai taka leda a kakar wasanni mai zuwa a Saudiyya inda zai kulla ‘babbar’ yarjejeniya, kamar yadda wata majiya kan yarjejeniyar da ake yi ta bayyana.

“Bakin alkalami ya bushe game da Messi. Zai taka leda a Saudiyya a kakar wasanni mai zuwa” in ji majiyar da ta nemi a boye sunanta a ranar Talata.

Majiyar ta kara da cewa “Yarjejeniya ce ta gani ta fada. Tana da maiko sosai. Muna kammala wasu kananan abubuwa ne kawai.”

Da aka tambayi kungiyar PSG da Messi ke taka leda a yanzu, sai ta bayyana yana da kwantiragi tare da su har nan da 30 ga Yuni.

Wata majiya ta daban ta PSG ta bayyana cewa “Idan kungiyar ta so sabunta yarjejeniyarta, da tuntuni an yi hakan.”

Ya bi sahun abokin hamayyarsa Ronaldo

A makon da ya gabata ne kungiyar PSG mallakin dan kasar Qatar ta dakatar da Messi mai shekara 35 bayan tafiyar da ya yi zuwa Saudiyya ba bisa ka’ida ba a matsayin jakadan yawon bude ido.

Ana sa ran isar Messi zuwa kasar da ke da arzikin mai wanda hakan ya biyo bayan Cristiano Ronaldo wanda ya tafi kungiyar Al Nassr ta Saudiyya bayan gwaggwabar yarjejeniya a watan Janairu.

Yarjejeniyar da Ronaldo ya sanya hannu a kai ta kai dala miliyan 439, wadda ta sanya shi zama dan wasan da ya fi kowanne karbar albashi kamar yadda Mujallar Forbes ta sanar.

TRT World