Zuwa yanzu, Mohamed Salah ya ciyo wa Liverpool ƙwallaye 223 cikin wasanni 367. / Hoto: Reuters

A gasar Firimiya ta Ingila, Liverpool ta kafa ratar zunzurutun maki 8 a saman tebur, bayan wassanin mako na 12 da aka kammala a ƙarshen makon jiya.

Wannan ya sa kulob ɗin ya ja hankalin masu bibiyar gasar, musamman ganin babbar abokiyar hamayyarsa, Manchester City tana fuskantar ƙalubale. Ga abubuwa uku da ake tattaunawa a kai.

Mohamed Salah ne zuciyar Liverpool

A wasan Lahadin nan da Liverpool ta buga a gidan Southampton, Mohamed Salah ne ya ceto ƙungiyar bayan da ya rama ƙwallo guda sannan ya ci ta uku a minti 83 da wasan inda aka tashi suna da ci 3-2.

Wannan na nufin Salah ne ya taimaka Liverpool ta tsallake barazanar da ta sanya wankin hula ya kai ta dare. Shi ma Salah sai a bugun ɗurme ya samu damar cin ƙwallon da ta hana su ɓarin maki biyu a wasan.

Wannan ba shi ne karo na farko da Salah yake ceto ƙungiyarsa ba a kakar bana, kuma a wannan wasan da ya gabata, 'yan wasan Liverpool irinsu Ibrahima Konate da Virgil van Dijk sun yi ta kwafsawa.

Zaratan Liverpool na shirin tafiya

Ko Salah, da Virgil van Dijk, da Trent Alexander-Arnold za su ci gaba da zama a Liverpool? Batun kwantiragin Mohamed Salah a Liverpool ya taso bayan da ɗan wasan ya faɗi wani abu da ya ja hankalin masoya Liverpool, kan makomarsa a ƙungiyar.

Salah ya ce ƙafafunsa sun fi kasancewa 'a waje sama da a cikin' ƙungiyar, inda kuma ya ce har yanzu ba a masa tayin sabuwar kwantiragi a ƙungiyar ba, ga shi kuma shi ne wanda ya fi kowa ɗaukar albashi a halin yanzu.

Salah ya furta hakan ne bayan wasan Liverpool da Southampton, inda aka ambato wata majiya tana faɗa wa The Athletic cewa tattaunawa da wakilin Salah, Ramy Abbas, tana 'kankama' kuma ana samun 'cigaba'.

Baya ga Salah, akwai kuma batun abokan wasansa irinsu Virgil van Dijk da Trent Alexander-Arnold waɗanda kwantiraginsu za ta ƙare a bazara mai zuwa, kuma har yanzu ba a ba su sabuwar kwantiragi ba.

Liverpool ta kama haryar lashe kofi?

Shafin Goal ya ambato tsohon ɗan wasan Manchester City, Sergio Aguero yana mai cewa tazarar da Liverpool ta samu a yanzu ta maki takwas a saman taebur, ba shi da 'wani tasiri', wato ba zai yi ƙarko ba.

Aguero ya ce akwai sauran tafiya a batun wa zai lashe gasar ta Firimiya, inda yake ganin tawagar Man City ta Pep Guardiola za ta iya sake yin ba-zata, wajen farfaɗowa ta ɗauki kofin.

Aguero yana cikin tawagar City da ta lashe Firimiya a ranar ƙarshe ta gasar a 2012, bayan samun nasara wuce Manchester United a yawan jimillar ƙwallaye, duk da cewa sun ƙare da maki daidai.

A yanzu dai Liverpool ta yi fintinkau da maki 31, kuma ƙungiyar da ke biye da ita, Man City na da maki 23. Liverpool ta samu wannan nasarar ne bayan Tottenham ta doke City har gida da ci 4-0.

TRT Afrika