Rahotanni daga Camp Nou gidan Barcelona na cewa Lamine Yamal zai ci gaba da kasancewa cikin 'yan kallo, yayin da ƙungiyar za ta karɓi baƙuncin Brest ta Faransa a gasar Zakarun Turai da za a dawo bugawa a maraicen yau.
Barca wadda ke saman teburin LaLiga, za ta yi rashin matashin ɗan wasan kasancewar bai halarci atisayen ƙungiyar ba na Litinin, inda aka tabbatar da cewa ba zai buga wasansu na yau Talata da za su yi a gida ba.
Haziƙin ɗan wasan ya samu rauni a idon sahunsa, wanda ya tilasta masa ƙauracewa wasanni biyu da Barca ta buga a gasar La Liga tare da Real Sociedad da kuma Celta Vigo.
A wasan farko babu Yamal wanda aka ce zai yi jinyar mako biyu zuwa uku, Barca ta sha kashi a hannun Real Sociedad da ci ɗaya mai ban haushi, inda kuma suka yi kunnen doki a wasansu da Celta Vigo da ci 2-2.
Rashin Yamal mai shekaru 17 a tawagar ya yi tasiri kasancewa sanda yana nan, Barca ta buga wasanni bakwai inda ta samu nasara a dukkansu.
Kafin tafiyarsa jinya, Lamine Yamal ya ciyo wa ƙungiyarsa ƙwallo shida da tallafin ƙwallo takwas a duka gasanni, tun fara kakar nan ta 2024-25.
Man City na neman farfaɗowa
An ambato kocin Manchester City, Pep Guardiola yana jan kunnen 'yan wasansa kan cewa dole su ba da hankalinsu kacokan ga tawagar, yayin da za su karɓi baƙuncin ƙungiyar Feyenoord a gasar Zakarun Turai da za a buga yau Talata.
Man City na fatan kawo ƙarshen raunin da take fama da shi, bayan ta buga wasanni biyar a jere ana lallasa ta. A wasansu na ƙarshe Tottenham ta doke su a gida da ci 4-0 a gasar Firimiya, ranar Asabar.
A tarihin jagorancinsa, Guardiola bai taɓa yin rashin nasara sau biyar a jere ba tun 2006, sai a wannan karon. Wannan ya sanya ana kallon wannan lokaci a matsayin mafi girman ƙalubale ga kocin.
Man City tana fama da rashin zaƙaƙuran 'yan wasanta da suke fama da jinya, cikinsu har da zakaran kyautar Ballon d'Or ta bana, Rodri, da kuma Ruben Dias, da Mateo Kovacic, da Jeremy Doku, da kuma Oscar Bobb.
Guardiola ya faɗa ranar Litinin cewa "Duba da irin nasarorin da muka samu, yana da wuya mu riƙe wannan matsayi, shi ya sa ba na damun kaina. Wannan ne ya sa nake buƙatar jajircewar 'yan wasana".
Manchester City na mataki na 10 cikin 36 a teburin gasar Zakarun Turai, inda take da maki bakwai daga wasanni huɗu, inda ta gaza shiga rukunin samun cancantar wucewa matakin gaba kai-tsaye, saboda ƙarancin maki biyu.
Duk da cewa Feyenoord da za su kara da City a yanzu tana mataki na 21 a teburin, rashin tagomashin City ya sanya za a zuba wa wasan na yau ido don ganin ko za su farfaɗo daga raunin da suke fama da shi.