A karon farko cikin shekara 21 kwamitin bayar da kyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa ta duniya wato Ballon d’Or ya fitar da jerin 'yan wasa 30 da za su fafata don neman kyautar amma ba tare da Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo a cikinsu ba.
Tun shekarar 2003 kwamitin yake sanya sunayen shahararrun 'yan wasan biyu a cikin jerin masu neman kyautar.
Ɗan wasan Portugal Ronaldo, wanda ya lashe kyautar sau biyar, ba ya cikin jerin waɗanda suka fafata a neman kyautar a bara, yayin da Messi, wanda ya karɓi kyautar sau takwas, bai samu shiga jerin ba a bana duk da cewa Argentina ce ta lashe kofin Copa America a wannan shekarar.
Sifaniya, ƙasar da ta ɗauki kofin Euro 2024, na da 'yan wasa shida da aka fitar da jerin sunayensu don lashe kyautar, ciki har da ɗan wasan Barcelona mai shekara 17 Lamine Yamal, da Nico Williams, Alejandro Grimaldo, Dani Olmo, Rodri da Dani Carvajal wanda ya lashe Gasar Zakarun Turai a Real Madrid.
Ga jerin sunayen 'yan wasan da ka iya lashe kyauta:
- Jude Bellingham (Ingila, Real Madrid)
- Hakan Çalhanoğlu (Turkiyya, Inter)
- Dani Carvajal (Sifaniya, Real Madrid)
- Rúben Dias (Portugal, Manchester City)
- Artem Dovbyk (Ukraine, Dnipro / Girona / Roma)
- Phil Foden (Ingila, Manchester City)
- Alejandro Grimaldo (Sifaniya, Bayer Leverkusen)
- Erling Haaland (Norway, Manchester City)
- Mats Hummels (Jamus, Borussia Dortmund)
- Harry Kane (Ingila, Bayern Munich)
- Toni Kroos (Jamus, Real Madrid)
- Ademola Lookman (Nijeriya, Atalanta)
- Emiliano Martínez (Argentina, Aston Villa)
- Lautaro Martínez (Argentina, Inter )
- Kylian Mbappé (Faransa, Paris Saint-Germain / Real Madrid)
- Martin Ødegaard (Norway, Arsenal)
- Dani Olmo (Sifaniya, Leipzig / Barcelona)
- Cole Palmer (Ingila, Manchester City / Chelsea)
- Declan Rice (Ingila, Arsenal)
- Rodri (Sifaniya, Manchester City)
- Antonio Rüdiger (Jamus, Real Madrid)
- Bukayo Saka (Ingila, Arsenal)
- William Saliba (Faransa, Arsenal)
- Federico Valverde (Uruguay, Real Madrid)
- Vinícius Júnior (Brazil, Real Madrid)
- Vitinha (Portugal, Paris Saint-Germain)
- Nico Williams (Sifaniya, Athletic Club)
- Florian Wirtz (Jamus, Bayer Leverkusen)
- Granit Xhaka (Switzerland, Bayer Leverkusen)
- Lamine Yamal (Sifaniya, Barcelona)