A shekaru uku yana riƙe da Feyenoord, Arne Slot bai taɓa rashin nasara sau biyu a jere ba. / Hoto: AFP

Ana dakon ayyana Arne Slot a matsayin wanda zai karɓi ragamar horar da Liverpool ta Ingila a hukumance, kocin wanda a yanzu yake horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Feyenoord da ke Rotterdam a ƙasar Netehrlands, ya fara yin bankwana da masoya.

An ruwaito cewa, yayin da wasa biyu suka rage masa ya jagoranci Feyenoord, Slot ya doge kan cewa ba a naɗa shi kocin Liverpool ba a hukumance. Amma kuma ya ce zai tuntuɓi Klopp don shawara game da jagorancin Liverpool.

Slot ya ambata haka ne bayan kammala wasan da Feyenoord ta doke PEC Zwolle da ci 5-0. An kuma gan shi yana gaisawa da magoya bayan kulob ɗinsa, a wani yanayi da ya yi kama da na bankwana ga masoya.

Da yake zantawa da manema labarai, Slot ya ce, "Tamkar ina bankwana ne da masoya? Na yadda da hakan, cewa kamar hakan ne ka faruwa saboda maganganun da ake ji a jaridu, ana ganin tafiya zan yi. E abu ne da za mu iya faɗa".

Ya ƙara da cewa, “Zan koma Liverpool? Idan sanarwa a hukumance ta zo, na tabbata ɗari bisa ɗari can zan tafi."

Game da ko zai nema shawarar Klopp idan ya isa Liverpool, Slot ya ce, "Ina ganin hakan daidai ne idan ka koma sabon kulob, kuma idan Liverpool ne, daidai ne na ka tuntuɓi tsohon koci".

Kocin Liverpool a yanzu, Jurgen Klopp ya riƙe ƙungiyar tsawon shekaru tara, kuma a ƙarshen kakar bana ne zai bar ƙungiyar kamar yadda aka ambata a watannin baya.

Slot ya jagoranci Feyenoord kakar wasanni uku, inda a bara ya ci gasar Erdivisie, yayin da a bana suka zo na biyu bayan da PSV ta lashe kofin. Slot ya taɓa kai Feyenoord wasan ƙarshe na gasar Europa Conference.

Idan ta tabbata Arne Slot ya gaji Klopp, tuni ya bayyana abubuwan da zai yi wanda ya haɗa da tuntuɓar koci mai barin gado, Jurgen Klopp, don samun shawarwari kan jagorancin Liverpool.

TRT Afrika