Zuwa yanzu, Vinicius ya ci ƙwallaye 8 a LaLigar bana, yayin da Mbappe ya ci ƙwallaye 6. / Hoto: AFP

Rahotannin daga Real Madrid na cewa koci Carlo Ancelotti 'ba zai sauya komai' a ƙungiyarsa ba, don tunanin taimaka wa Kylian Mbappe ya samu mafita daga ƙamfar cin ƙwallo da yake fama da ita.

An ruwaito cewa Carlo Ancelotti ya yanke wannan hukuncin ne dangane da batun sauya wa Vinicius Jr lamba daga matsayinsa na ɗan wasan gaba da ke aiki daga gefen hagu.

Wannan na nufin cewa Ancelotti ya ba da fifiko kan Vinicius, maimakon Mbappe, a faɗan neman matsayi mafi kyau wanda ke gudana tsakanin zaratan 'yan wasan.

Tun bayan barin Paris Saint-Germain ta Faransa inda ya zo Madrid, kulob ɗin da ya ci burin bugawa wasa, Mbappe yana buga wasa ne daga tsakiya, kasancewar gefen hagu da ya saba takawa a baya ya tarar da Vinicius a kai.

An yi ta tunanin ko Madrid za ta sauya salon tawagarta, don bai wa 'yan wasansu na gaba damar daidaita kansu da kyautata ƙwazonsu.

Sai dai kamar yadda shafin Goal ya ambato Diario AS na cewa, Ancelotti ya yanke hukuncin cewa 'ba zai sauya komai' ba a tawagar tasa, don daɗawa Mbappe.

Fifita Vinicius

Ancelotti ya ɗauki wannan mataki ne saboda gudun ɓata tagomashin Vinicius, kasanscewar kocin yana ganin Vini shi ne ɗan wasan da 'ya dogara da shi wajen jagorancin ƙungiyar'.

Zuwa yanzu a Madrid, Mbappe ya ci ƙwallaye takwas cikin wasanni 16 da ya buga a duka gasanni, inda ƙwallaye uku cikinsu ya ci su ne daga bugun ɗurme.

Sai dai bai ci ƙwallo ko guda ba a wasanni huɗu da ya buga Madrid a baya-bayan nan, wanda ke nuni da rashin tagomashinsa a kakar bana.

A halin yanzu, Real Madrid tana ƙasa da Barcelona a saman teburin LaLiga da maki shida, duk da tana da kwantan wasa guda.

Za su kara da Leganes ranar Lahadi, inda ake fatan Mbappe zai nuna rawar gani, kasancewar ya samu hutu saboda bai buga wa ƙasarsa wasa ba a lokacin wasannin ƙasa-da-ƙasa da aka buga a makonnin nan.

TRT Afrika