Rahotannin sun bayyana cewa shugaban hukumar La Liga da kansa Javier Tebas, yana dakon binciken yiwuwar dawowar Messi / Hoto: AP

Rahotannin sun nuna cewa Barcelona za ta gina gidan adana tarihi na karrama Messi, don ta tara kudin sayo dan wasan a kakar sayen ‘yan wasa da ke zuwa nan da ‘yan makonni.

Za a gina gidan tarihin ne dab da filin wasan Barcelona na Camp Nou, don karrama Lionel Messi wanda gwarzon dan wasan Barcelona ne wanda ya buga mata wasa tsawon shekara 21 a baya.

Watanni kadan ne dai suka rage wa Messi a kwantiraginsa na PSG, kuma ana rade-radin cewa kulob din na Faransa ya shirya sakin shahararren dan wasan.

Ana kyautata zaton cewa Messi zai koma tsohon kulob dinsa, duk kuwa da rahotannin da ke nuna wasu manyan kungiyoyin kwallo suna burin saye shi da zarar ya fito kasuwa.

Jami’an kungiyar su kansu sun bayyana burinsu na dawo da Messi zuwa Camp Nou, inda a ‘yan kwanakin nan suka ce tattaunawa tana ci gaba da gudana da wakilan dan wasan.

Sai dai alamu sun nuna Barcelona tana fama da matsalar kudi, wanda ke nufin wannan yunkuri na gina gidan tarihi don karrama Messi ba zai ba da mamaki ba.

Manuniya

Rahotannin sun bayyana cewa shugaban hukumar La Liga da kansa Javier Tebas, yana dakon binciken yiwuwar dawowar Messi.

Shafin Goal.com ya ambato gidan jarida a Sifaniya na AS ya bayyana cewa wata hanyar tara kudin kawo Messi ita ce mayar da tsohuwar hedikwatar makarantar matasa ta kwallon kafa, La Masia, da ke kusa da Camp Nou, zuwa gidan tarihin karrama Messi.

Kuma rahotannin sun nuna tuni aka fara tattaunawa da kamfanin sadarwa na Telefónica, don ganin yiwuwar aiwatar da wannan shiri.

Ana sa ran gidan tarihin zai kasance na zamani, wanda zai nuna 'mutum-mutumin Messi da za a iya suranta mu’amala da shi'. Hakan zai iya janyo ‘yan yawon bude ido da masoya, wanda zai samar da kudin-shiga.

Karin damar samar da kudi ta hanyar lasisin talabijin da talla, ita ake ganin za ta janyo shugaban na La Liga zai amince da sayo Messi.

TRT Afrika