Mohamed Elneny na ƙungiyar Arsenal ya buɗe wani ɗakin ibada a ginin filin wasan kulob ɗin, wato Emirates Stadium, wanda ke birnin Landan.
Elneny wanda ɗan wasan tsakiya ne ɗan asalin Masar, ya shiga Arsenal ne bayan ya baro kulob ɗin Basel na Switzerland a shekarar 2016.
Ɗakin ibadar na amfanin addinai mabambanta ne, ta yadda mai gudanar da wata ibada zai samu wajen da zai keɓanta ya yi ibada cikin natsuwa.
"Ina alfahari da cewa na buɗe wannan ɗakin ibada na ‘yan wasa a filin wasa na Emirates Stadium," cewar Elnany a shafinsa na X ranar Litinin.
Ya ƙara da cewa, "Samun wannan ɗaki don yin ibada ko wuridi zai sauya rayuwar ‘yan wasan Arsenal da za su shigo kulob ɗin nan gaba. Ina godiya ga ma’aikata da duk wanda ya taimaka na cimma wannan."
Shekarun Elnany 31 a duniya, kuma a baya ya taɓa buga wasa a ƙungiyar Besiktas ta Turkiyya.