Kazalika kwamitin ya ce dole ne Ronaldo ya biya tarar riyal 10,000 ($2,666) ga Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafar Saudiyya, da kuma riyal 20,000 ($5,332) ga ƙungiyar Al-Shabab bisa ƙorafin da ta shigar. / Hoto: Reuters

An dakarar da Cristiano Ronaldo daga buga wasa ɗaya saboda samunsa da laifin rashin ɗa'a a fafatawar da Al Nassr ta doke Al Shabab da ci 3-2, in ji Kwamitin Yaƙi da Rashin Ɗa'a na Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafar Saudiyya (SAFF) ranar Laraba.

Bidiyoyin da aka riƙa watsawa a soshiyal midiya sun nuna yadda ɗan wasan na Portugal ya toshe kunnuwansa sannan ya riƙa saka hannayensa a kusa da mazakutarsa, a wani mataki da ake gani tamkar cin-fuska ne ga magoya bayan ƙungiyar da suka fafata da ita.

Kazalika kwamitin ya ce dole ne Ronaldo ya biya tarar riyal 10,000 ($2,666) ga Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafar Saudiyya, da kuma riyal 20,000 ($5,332) ga ƙungiyar Al-Shabab bisa ƙorafin da ta shigar. Sai dai yana iya ɗaukaka ƙara.​​​​​​​

Ɗan ƙwallon wanda sau biyar yana lashe kyautar Ballon d'Or ya tafi Al-Nassr daga Manchester United a bara, kuma tun daga wancan lokacin ne wasu manyan ƴan wasa suka bi sawunsa inda suka tafi ƙungiyoyin ƙwallon kafar Saudiyya.

AA