Wani gwaji da aka yi wa ɗan wasan Chelsea, Mykhailo Mudryk ya nuna cewa yana ta'ammali da ƙwayoyin ƙara kuzari, inda hakan ya janyo hukumar ƙwallo ta Ingila ta dakatar da shi daga harkar ƙwallo.
Mudryk ɗan asalin Ukraine ne mai shekaru 23, kuma yana buga wasa a Chelsea a matsayin ɗan wasan gaba mai kai farmaki daga gefe.
Tun ranar 28 ga Nuwamba Mudryk bai buga wasa ba saboda gwajin da ya nuna ya sha ƙwayar ƙara kuzari. A wasansa na ƙarshe ya ci ƙwallo a gasar Europa Conference wanda Chelsea ta doke Heidenheim.
Dakatarwar ta haramta wa Mudryk shiga duka wata harka ta ƙwallo har zuwa lokacin da za a yanke hukunci na gaba a kansa.
A baya an yi ta cewa rashin lafiya ce ta hana Mudryk buga wasa, amma yanzu ta tabbata zargin shan ƙwaya ne ya hana koci Enzo Maresca saka shi a wasa.
Ƙwayar Meldonium
A cewar jaridar The Athletic, gwaji ya nuna cewa ɗan wasan ya sha ƙwaya nau'in Meldonium, wadda magani ne da aka saba amfani da shi don neman waraka daga cutukan zuciya kamar angina, amma yana taimakawa wajen ƙara kuzari.
Sanarwar hukumomin Chelsea dai na cewa, “Ƙungiyar ƙwallo ta Chelsea tana tabbatar da cewa hukumar ƙwallo ta Ingila kwanan nan ta tuntuɓi ɗan wasanmu Mykhailo Mudryk game da abin da ta gano daga gwajin fitsarinsa".
Duk da Chelsea ta ce tana goyon bayan gwajin da hukumomi ke yi kan 'yan wasa lokaci-lokaci, Mudryk ya musanta yin amfanin da ƙwayoyin ƙara kuzari da aka haramta, da gangan.
A wata wallafa da ya yi a soshiyal midiya, Mudryk ya mai da martani kan labarin inda ya ce: “Ina tabbatar da cewa an sanar da ni cewa samfurina da na bai wa FA an gano akwai sinadarin da aka haramta a cikinsa".
“Wannan ya zo min da matuƙar mamaki saboda ban taɓa amfani da wani magani da aka haramta ba da gangan, ko don na karya doka. Kuma ina aiki tare da ƙungiyata don bincike kan yadda hakan ta faru."
Mudryk ya nanata cewa bai aikata wani laifi ba, kuma yana fata zai dawo filin wasa da zarar an wanke shi daga laifi.
Mudryk ya zo Chelsea ne kan kuɗi dala miliyan 113 a Janairun 2023, inda ya sanya hannu kan kwantiragin shekara takwas. Ya buga wa Chelsea wasanni 73 inda ya ci ƙwallaye 10.