Kocin Tottenham Ange Postecoglou ya sanar da cewa ƙungiyar ta dakatar da ɗan wasanta Yves Bissouma, daga wasansu na farko a kakar bana, wanda za su buga ranar Litinin.
Kocin ya bayyana cewa Tottenham ta dakatar da Bissouma dangane da bidiyonsa da ya yi yawo, inda aka ga yana shaƙar gas ɗin nitrous oxide, wanda aka fi sani da gas mai sa dariya ko Laughing Gas da Turanci.
Bissouma wanda ɗan asalin Mali ne, ya wallafa bidiyo a Snapchat wanda ya nuna kansa yana zuƙar gas mai saka dariya, yana cikin mota ƙirar limousine kuma yana sheƙa dariya.
An wallafa bidiyon ana sati guda kafin Tottenham ta fara buga wasanta na farko a Gasar Firmiya ta bana, inda za su buga da Leicester a ranar Litinin.
Ƙungiyar ta ɗauki mataki kan Bissouma, inda ta dakatar da shi daga buga wasa ɗaya, duk da dai koci Postecoglou ya ce dakatarwar za ta iya wuce hakan.
Postecoglou ya ce, "Bayan dakatarwar, akwai buƙatar (Bissouma) ya yi abin da zai sa a sake gina aminci da shi, da kuma tsakanin Biss da ni, da kuma ƙungiyarmu. Abin da ya kamata ya yi ƙoƙarin yi kenan daga yanzu, kafin ya sake samun wata dama".
"Yana da alhakin daraja ƙungiyarmu, yana da alhaki kan abokan wasansa, yana da alhaki kan masoya da duk wanda ke da alaƙa da kulob ɗin, amma ya gaza a wannan aikin. Dole a yi hukunci kan haka," cewar kocin a taron manema labarai.
Ƙungiyar Tottenham ta kammala gasar Firimiya a mataki na biyar a kakar bara, inda a yanzu take fatan yin nasarar shiga cikin huɗun farko a teburin gasar, don ya buga gasar Zakarun Turai ta baɗi.