A watan Agustan 2022 masu kutse sun samu damar yin kutse a shafin intanet na babban bankin kasar Afirka ta Kudu/Photo AA

Bayan da ofishin jakadancin Nijeriya da ke Afirka ta Kudu ya gargadi 'yan Nijeriya mazauna Afirka ta Kudu game da hatsarin nuna murna idan Nijeriya ta yi nasara a wasan kasashen biyu a gasar AFCON, Afirka ta Kudu da mayar da martani.

Tun da fari, Nijeriya ta yi wa 'yan kasarta gargadin ne don su kauce wa farmakin nuna ƙyamar baki da aka gani a baya, tana mai nuna tsoron takalo masoya tawagar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu, idan aka ce kasarsu ba ta samu galaba ba.

Sai dai a martanin da ta mayar, gwamnatin Afirka ta Kudu ta soki gargadin a matsayin "mara dalili".

Ofishin Hulda da kasashen waje na Afirka ta Kudu ya bayyana cewa babu tarihin faruwar farmaki sakamakon wasan ƙwallo tsakanin kasashen biyu.

Da ma dai akwai dadaddiyar hamayya tsakanin Nijeriya da Afirka ta Kudu a fagen kwallon kafa, inda a wannan karo kasashen biyu za su kece raini a wasan dab da na karshe na gasar AFCON da ke gudana a kasar Ivory Coast.

Hakan ya sa Afrika ta Kudu ta yi Allah wadai ta gargadin da Nijeriya ta yi game da 'yan kasarta da ke zama a kasar tasu.

TRT Afrika