Hukumar Kwallon Kafa ta nahiyar Afirka, CAF za ta dauki matakai don magance abin da ta kira da "yawaitar dabi'u marasa dacewa" a ayyuka 'yan jaridu da ke daukar gasar cin kofin Afirka na AFCON da ke gudana a Ivory Coast.
Sanarwar CAF na zuwa ne bayan fuskantar faruwar irin wannan halayya, wadda ta hada da fada tsakanin 'yan rahoto yayin nuna murnar cin kwallo a rumfar 'yan jaridu.
CAF ta sanar ranar Juma'a cewa ta zauna da kwamitin shirya gasar da kuma 'yan sanda don fito da tsarin warware matsalar. Haka nan hukumar ta kai koke gun gidajen jaridu da suka turo wakilansu gasar.
“Daga yanzu duk dan jaridar da ya nuna murna irin yadda bai dace ba, ko ya zagi abokan aikinsa, jami'an tsaro za su fitar da shi kuma a karbe takardar izininsa. Haka ma duk dan jaridar da ya shiga fada ko ya kai hannu.” a cewar hukumar CAF.
Kalaman zagi
Hukumar ta CAF ta kuma ce haramun ne daukar bidiyon wasa daga rumfar 'yan jarida, da nuna wasa ta hanyar kwaranyen bidiyo kai-tsaye a zauren haduwa da 'yan wasa. Kuma ta ce ba za ta lamunci amfani da kalaman zagi ga masu horar da 'yan wasa ko 'yan wasa.
Wasu 'yan jarida daga Ghana sun yi cacar baki da tawagar 'yan wasan Ghana bayan da aka fitar da tawagar. Hakan ya janyo wasu 'yan wasan suna kaurace wa zauren tattaunawa da 'yan jarida, har jami'an tsaro su musu rakiya zuwa motarsu.
Ranar Laraba ne Kungiyar Duniya ta 'Yan Jaridun Wasanni ta yi Allah-wadai da 'yan jaridun da suka nuna dabi'ar rashin kyautawa a gasar ta AFCON ta wannan shekara.
Kungiyar ta koka kan yadda aka samu “fada a filin wasa, da kai hari, da zagi, da kuma yadda wasu suke nuna rashin mutuntawa".
Yin karaji lokacin murna
An ga 'yan rahoto da suke da izinin aikin jarida wajen gasar suna sanye da rigunan tawagar kasarsu, kuma suna nuna goyon baya ga tawagar kasarsu yayin wasa, suna kuma yin kara lokacin murnar cin kwallo ko cin wasa.
Haka nan an samu cacar baki tsakanin 'yan jarida da ke kokarin shiga motar zuwa kallon wasa, sannan an samu takun-saka tsakanin 'yan jarida daga Guinea da Senegal kafin wasansu na matakin rukuni, da kuma wakilai 'yan Maroko da na Afirka ta Kudu yayin wasansu ranar Talata.