Matasan na kungiyar 'One Bike' sun fara wannan kokari a 2018. Hoto: TRT Afrika

Daga Ma'aikaci

Asabar din farkon kowacce shekara ce ranar da matasan da aka fi sani da kungiyar 'One Bike' ta sanya wa mambobinta don aikin tsaftar muhalli.

Suna kwashe kwalabe a ciki da kewayen Moshi, babban birnin yankin Kilimanjaro na arewacin Tanzania.

Suna kuma amfani da wannan aiki wajen wayar da kan mutane game da illar robobi wajen gurbata muhalli.

"Mun fahimci cewa roba makiyiyar muhallinmu ce, hakan ya sanya muke son al'umma su agaza mana don mu yi aikin tare," in ji mai fafutukar kare muhalli Hillary Matemu wadda na daga cikin 'yan wannan kungiya.

Mambobin kungiyar suna zagayawa daga wannan waje zuwa wancan, suna hawa kekuna, dauke da jakunkuna a bayansu suna tattara kwalaben roba da suka kai wa kamfanoni don sake sarrafa su.

Masu tsaftace Kilimanjaro na kwashe kwalaben roba kilo 35 zuwa 50 a kowacce ranar aikin.. Photo: TRT Afrika

A 2018 suka fara wannan aiki tare da ba shi sunan "Zagayen Sake Sarrafawa" don jan hankalin mazauna yankunan da 'yan yawon bude ido s hada kai da su wajen kwashe kwalaben roba da aka zubar da su a ko'ina.

A kowacce ranar aikin, suna tattara kwalaben roba kilo 35 zuwa 50, ya danganta da adadin mutanen da suka fito aikin gayyar.

Mambobin kungiyar sun fara wannan yunkuri a wani karamin shagonsu da suke sayar da kekuna na hannu.

Suna tallata wannan aiki nasu ta shafukan sada zumunta, suna gayyatar mutane da su zo su tai tare, suna kuma samun karin jama'a.

Kungiyar 'One Bike' a yanzu na samarwa da masu aikin sa kai kekuna da hulunan kwano da jakunkuna da safunan hannu don yin aiki.

Gwamnati ta san da zaman kungiyar ta One Bike masu tsaftace muhalli. Hoto: TRT Afrika

Ana zabin hanyoyi ko yankunan da za a je don tsaftacewa duba da kyawu da kayatarwar Kilimanjaro da Moshi inda aikin zai zama mai kayatarwa sosai, ya zama kamar wayar da kan jama'a kan muhimmancin yankin wajen yawon bude ido.

Gwamnatin yankin Kilimanjaro ta san da zaman wannan kungiya a matsayin masu tsaftar muhalli a hukumance da ke kwashe kwalaben roba da mutane suka zubar a yayin gasar tsere da Kilimarathon.

Ana yin wannan aiki a ranar Asabar din farkon kowanne wata. Hoto: TRT Afrika

Mai fafutukar kare muhalli Hillary Matemu na cewa irin wannan aiki bai kamata ya zama na Kungiyar One Bike kadai ba. Kowa ya kamata ya shiga aikin.

TRT Afrika