Tauraron wakoƙin Afrobeats daga Nijeriya Davido, mai shekaru 31, ya yi tattaki a dandamali nuna ado na taron makon kwalliya na jihar Legas da ke yankin Kudu maso Yammacin Nijeriya na shekarar 2024 a ƙarshen makon da ya gabata.
Mawaƙin ya sanya kayan gargajiyar da Ugo Monye ya tsara, kuma shi ne ya ƙawata shi a lokacin bikin aurensa da Chioma Rowland a watan Yuni 2024.
Kazalika shi ma Monye ya yi tattaki tare da Davido a dandanmalin taron baje-kolin kayayyakin ƙwaliyyar.
Davido dai ya sanya wata doguwar riga mai launin ruwan ƙasa daga kai har ƙafa, tare da wata sarƙar wuya ta gargajiya da ta shiga da kayan da ya saka, yana mai riƙe da wata sandar tafiya.
Rawar da masana'antar ƙwalliya da ado ta Nijeriya ke takawa
Baya ga Monye, akwai sauran wasu fitattun masu tsara kayayyakin ado da kwalliya da suka baje-kolin ayyukansu a wajen wadanda suka haɗa da Imad Eduso, da Maliko,da Pettre Taylor, da kuma Oshobor.
Makon Kwalliya na Legas wani shirin taro ne da ke taka muhimmiyar rawa a masana'antar kayan ƙwalliya da ado a Nijeriya da Afirka.
Taron yana haɗa 'yan kasuwa da masu saye da kuma kafofin yada labarai dana nishaɗi don kallon tarin baje kollin zanen kayayyaki a taron na kwanaki hudu a birnin kasuwanci na Nijeriya, wato jihar Legas.
An gudanar da taron na bana ne daga ranar 23 zuwa 27 ga watan Oktoba.
Nuna ƙwalliya da adon kayayyaki tare da gabatar da shirye-shirye na nishaɗantar suna daga cikin ayyukan da ake gabatarwa a taron na kowane shekara.