Daga Mazhun Idris
A wani yabon da ta yi wa daya daga cikin tsoffin 'yan wasanta, Chelsea ta bayyana fitaccen dan wasan Nijeriya John Mikel Obi a matsayin wanda yake nuna bajinta da kwazonsa a "muhimmin lokaci".
Ba shakka dan wasan ya cancanci wannan suna a matsayin babban dan wasan tsakiya wanda a yanzu ya koma bayan fage ta shirin Podcast dinsa mai suna ''Obi One''- inda yake yada shirye-shirye da suka shafi kwallon kafa, kuma ya samu karbuwa sosai a wajen jama'a.
A yammacin ranar 18 ga watan Disamba, duniyar kwallon kafa ta girgiza kan wani shiri da Obi One ya gabatar inda ya karbi bakuncin Jose Mourinho dan kasar Portugal, kuma kocin AS Roma ta Italiya.
Mourinho, wanda kafafen yada labarai ke kira “Special One”, ya yi wa kungiyoyin gasar Firimiya mummunar suka, inda ya caccaki Arsenal da Tottenham Hotspur da Manchester United, duk da cewa ya taba jagorantar kungiyoyi biyu daga cikinsu.
Obi, wanda ya yi ritaya daga buga kwallon kafa a watan Satumbar 2022, ya tara isassun bayanai da sirrin abubuwan da suka faru a manyan kungiyoyin Turai don tabbatar da cewa tattaunawarsa da Mourinho ta yi armashi.
Shirin ya bayyana alamar zuwan Obi a matsayin mai gabatar da shirye-shirye, makonni kadan bayan kaddamar da shirin Podcast na mako- mako na Obi One a ranar 30 ga watan Oktoba.
Watakila shi ya sa shirin ya ja hankali sosai saboda kama da wasan kwaikwayo nan mai suna "Obi-Wan Kenobi", wani fitaccen shirin fina-finai na Star Wars.
Ga Obi, wanda ya dauki nauyin gabatar da shirin tare da fitaccen kwararren masanin wasanni na Burtaniya Chris McHardy, makasudin shirin shi ne ya yi tattaunawa da taurarin kwallon kafa da manajojin kungiyoyin kwallon kafa da sauran masu ruwa da tsaki na manyan wasanni a duniya.
Tattaunawa mai jan hankali
Baya ga kwallon kafa, shirin yana nuna sirrin dakin saka kayan wasa da kuma wasu labaran da ba a bayyana ba . Tun da aka kaddamar da shirin a watan Oktoba, shirin na podcast ya yi fitowa bakwai da gyara biyu, kuma dukkansu sun ja hankalin miliyoyin mutane.
Ana samun shirin na podacst a manhajar Spotify da Apple Podcasts da Google Podcasts da kuma YouTube tare da wasu kafofi na intanet. Ko wane kashi na shirin yakan kai kasa da awa daya zuwa minti 120 .
A kashi na farko na shirin, Obi ya karbi bakuncin tsohon abokin wasansa a Chelsea John Terry, wanda ya taba kasancewa kyaftin din Ingila. Kashi na biyu ma ya karbi bakuncin wani gwarzon dan wasan Chelsea kuma tsohon kyaftin din Ingila, Frank Lampard.
Sauran shirye-shiryen sun karbi bakuncin Victor Osimhen, tsohon dan wasan Faransa Florent Malouda, da kuma tsohon dan wasan Italiya, Gianfranco Zola. Baya ga Mourinho, kocin da ya zanta da Obi shi ne Roberto Di Matteo.
Yabon masu sharhi
Bayan fitowar shirin a karo na bakwai da kuma kashi biyu na musamman, masu sharhi sun ji dadin shirin podcast din Obi One Podcast. Wasu na ganin shirin zai iya kamo wasu shirye-shirye da suka shahara irin su ESPN FC da Football Ramble da kuma That Peter Crouch Podcast.
Manyan gidajen jaridu sun ambato hirarraki daga shirin podacst din Obi One Podcast, kuma miliyoyin mutane a shafukan sada zumunta sun kalli gajerun bidiyon da aka yanka daga shirin.
Yayin da aka shiga sabuwar shekara, mutane suna sauraron sabbin shirye-shirye masu kayatarwa daga dan wasan Nijeriya da kuma masanin wasannin.
Ana yi wa shirin fata na gari, amma Obi, wanda ya taka leda a Stoke FC da Middleborough a Ingila, da kuma Trabzonspor ta Turkiyya, da kungiyoyin Norway da China, zai iya ba marada kunya.