Daga Sylvia Chebet
Ruwan sama na ban mamaki a sahara ya bar hotunan ruwa na gangarawa a kan yashi a kudu maso-gabashin Moroko, inda ya raya yanki mafi fuskantar karancin ruwan sama a yankin.
Wannan ruwa na ban mamaki ya baje tuddan yashi, tare da samar da lyukan da suka rike ruwa, a tsakanin kananan bishiyun kwakwa nan da can.
Manyan motocin da suka ziyarci saharar na dauke da 'yan yawon bude ido da mazuana yankin sun shaida wannan abin ta'ajibi.
"Mamakon ruwan saman da aka samu a baya-bayan nan a yankin Sahel da Sahara sun zama wani lamari da ba a saba gani ba da ke kara haske kan tasirin sauyin yanayi kan saukar ruwan sama a yankin." Houssine Youabeb na Hukumar Kula da Yanayi ta Moroko ya fada wa TRT Afrika.
Abin kallo a Sahara
"Asali dai, wadannan yankuna ba sa samun ruwan sama, inda ake samu a wani dan lokaci kankani."
Gwamnatin Morokko ta bayyana cewa kwanaki biyu na mamakon ruwan sama a Satumba ya haura wanda ake samu a shekara a yankuna da dama da ake ganin kasa da millimeers 250 a shekara, ciki har da Tata, daya daga yankunan da suka fi samun karancin ruwan sama.
"An dauki shekaru 30 zuwa 50 ba mu samu ruwan sam mai yawa irin haka ba a cikin gajeren lokaci," in ji Youabeb.
Mamakon ruwan saman da aka samu a tsakanin 6 da 9 ga Satumba da 19 da 22 ga watan na bayyana muhimmin sauyi da aka samu, in ji kwararru kan sha'anin sauyin yanayi.
Sun bayyana cewa yawan ruwan saman da aka auna ya zuba, ya kama daga 50mm zuwa 130mm a awanni 24 kawai, wand aya haura matsakaicin da aka saba gani a lokacin damina baki daya.
"Dadin dadawa, kadawar iska zuwa bangaren arewa wand aya kawo ruwan saman d aya haura 200mm a cikin awanni 48 a farkon wtaan Satumba, abu ne da ba a saba gani ba, sabod aya haura yawan ruwan da aka saba samu a irin wannan lokaci a wadannan yankuna."
Taurarun dan adam na NASA sun nuna ruwa na kwarara zuwa Tafkin Iriqui, shahararren tafki d ake tsakanin Zagora da Tata da yake a bushe kamas tsawon shekaru 50.
Ruwan saman da ba a saba gani ba
Irin wannan ruwan sama, wanda masana yanayi ke kamantawa da ruwan saman da ba a saba gani ba, na iya sauya yanyin yankin a watanni ko shekaru masu zuwa, a yayinda iska take rike danshi, tana janyo guguwa da iska.
"Sun taimaka wajen farfado da ruwan karkashin kasa da lokacin bazara, sun sake rayar da kwazazzabai, suna taimakon halittun da ke rayuwa a wajen," in ji Youabeb, yana mai tsokaci da cewa "Tafkin Iriqui .. ya sake cika, kuma madatsun ruwa irin su Qued Zaza ma sun cika makil."
Wuraren adana ruwa na yankin sun ciko sosai a watan Satumba.
Sai dai kuma, shekaru shida da aka fuskanci fari a jere ba a gama fahinmtar yadda ruwan na Satumba zai kawar da illar da aka samu daga tsawon lokaci na fari da rashin saukar ruwan sama a yankin.
Ruwan saman na ban mamaki ya yi ajalin mutane 20 a Morokko da Aljeriya, inda ya lalata amfanin gona da tirsasawa gwamnati raba kayan taimakon jinkai, har ma a yankunan da grgizar kasa ta shafa a shekarar bara.