An gudanar da bikin baje kolin fasahohi na Ghana wanda ke mai da hankali kan bikin fasahar zane-zane da al'adu da kuma yawon buɗe ido a kwanan nan a yankin Volta na ƙasar.
Bikin na kwanaki uku, wanda aka gudanar daga ranar 1 zuwa 3 ga watan Nuwamba, an soma shi ne a ranar Juma'a da jawaban ilimantarwa ga daliban fasahar zane-zane na garin Keta da Alonga – manyan wuraren yawon buɗe ido biyu da ke yankin Voita a ƙasar.
Bikin fasahohi na Tsadidi, wanda a yanzu ya kai shekara uku da aka soma, yana nufin yawon shakatawa a harshen Ewe. Glenn Samm, wani mai ba da labari ta hanyar zane-zane kana mai tallan ƙawa ne ya ƙirkire bikin.
Kimanin masu yawon bude ido miliyan 1.1 ne suka ziyarci Ghana a shekarar 2023, a cewar wata kiɗiddiga da aka fitar.
Taken bikin Tsadidi na bana a shekarar 2024 shi ne, "Gwajin Al'adu," inda aka baje kolin kayayyakin tarihi na yankin Volta.
Wasannin al'adu
An ƙarkare bikin na ranar Juma'a ne da zaman shan ɗumin wuta da ba da tatsuniya, sannan aka ɗora da tattakin fasahar zagaye garin Keta a ranar Asabar.
An baje kayayyaki da tufafin gargajiya da zane-zanen fasahohi akan hanyoyi da dai sauran wasannin al'adu a muzaharar da aka yi.
Bikin ƙarshe da aka gudanar a ranar Lahadi, an yi ciye-ciye a bakin teku inda aka baza abincin gargajiya iri daban-daban tare da kiɗe-ƙiɗe na gargajiya.
Ayyukan nishaɗi
"Biki yana haɗa mutane wuri ɗaya da kuma masu ba da tallafi zuwa bikin bisa ga mabambantan dalilai, ciki har da shaida irin al'adun gargajiya da ake da su,'' kamar yadda Glemn Samm ya bayyana a wata hira da kafar Grapic Showbiz ya yi da shi.
“Kamar dai yadda aka saba, bikin baje kolin fasahar Tsadidi yana ƙirkirar ayyukan nishaɗi ga mahalarta kana a wannan karon da aka gudanar da bikin an samar da shirye-shiryen nishaɗi daban-daban, inda aka fi mai da hankali kan fasahohi,'' in ji shi.
Glenn Samm, wanda ainihin sunansa shi ne Samuel Glenn Semakor, ya lashe lambar yabo ta Fashion Influencer na shekara na shirin Pulse Influencer a shekarar 2022.