A shekaru 21, mawaƙin ɗan Nijeriya, marubucin waƙa kuma mamallakin kamfanin harkokin waƙa ya bayyana ne a fagen waƙoƙin Afrika tare da daɗin bakinsa da daddaɗar murya, kuma tun sannan, wannan mawaƙin, ɗan baiwa, ya kasance mawaƙin Afrika mafi karɓuwa da ƙarfin faɗa-a-ji.
Sunan Wizkid na asali shi ne Ayodeji Ibrahim Balogun. An haife shi ranar 16 ga watan Yuli a shekarar 1990,a gundumar Surulere ta jihar Lagos, Cibiyar Kasuwancin Nijeriya.
Mahaifinsa shi ne Alhaji Muniru Olatunji Balogun, Musulmi kuma ɗan kasuwa ɗan siyasa da kuma mahaifiya Kirista, Jane Dolapo Balogun,wacce har ila yau, ƴar kasuwa ce kuma ita aka ce ta ba wa Wizkid cikakken goyon baya yayin da yake fafutikar zama tauraron waƙa.
Mahaifiyarsa ta rasu ranar 18 ga watan Agusta na shekarar 2023
Wizkid shi ne ɗan namiji ɗaya tilo a wajen mahaifiyarsa tare da ƴan uwa mata guda biyu, amma mahaifinsa yana da wasu matan guda biyu. Duka duka, Wizkid ya tashi tare da ƴan'uwa 12.
Wizkid ya fara waƙa yayin da yake ɗan shekara 11 da haihuwa a coci, yana waƙa tare da wasu abokansa na coci ƙarƙashin ƙungiyar da ake kira Glorious Five. Sun saki alibum kafin suka watse. Daga nan Wizkid ya fara amfani da sunan Lil Prinz har zuwa shekarar 2006.
Sannan ne ya gane cewa ya wuce ƙaramin yarima. Ya fara zuwa sutudiyo da ganawa da mawaƙa, kuma sai tsantsar baiwarsa ta fara bayyana.
Zuwa ƙarshen shekarun 2000, Wizkid yana aiki a matsayin mai taimaka wa mawaƙi - mawaƙin da ke waƙa tare da wani mawaƙin domin jawo hankalin masu kallo da sauraro. Ya yi aiki da mawaƙin raf, Kelz sannan ya yi amshi wa mawaƙin raf na Nijeriya MI.
A shekarar 2019, ya ƙulla wata yarjejeniyar waƙoƙi tare da kamfanin Empire Mates Entertainment (EME) wanda mawaƙi kuma marubucin waƙa Banky W ya mallaka.
A shekarar 2011, ya samu shuhura a hukumance da waƙarsa da ta yi shura "Holla at Your Boy".Wannan Ita ce fitacciya ƙwar-ɗaya daga jerin waƙoƙin alibam ɗin da ya yi a sutudiyo na farko mai suna "Superstar", kuma alibam ne da yake cike da waƙoƙin da suka yi shura - "Tease Me da Don't Dull" wasu misalai ne. Tun sannan, Wizkid ya zama gagarabadau.
A shekarar 2016, Wizkid ya yi shuhura duniya biyo bayan haɗin gwiwa da Drake a wata ƴar ƙwar-ɗaya da ta yi fice mai suna "One Dance", wacce ta zo ta ɗaya a jerin zafafan waƙoƙin Billboard na Amurka guda 100, sannan ta zo na ɗaya a jerin zafafan waƙoƙi a wasu ƙasashe 14.
Waƙar ta kafa tarihi da dama, ta sa Wizkid ya zama mawaƙin Afrobeat na farko da ya shiga kundin tarihi na Guinness Book of World Records a matsayin waƙa ta farko da aka kalla da saurara sau biliyan ɗaya a manhajar Spotify a watan Disamba 2016.
A 2022, mawaƙin ya sake kafa wani tarihin, da ya sayar da illahirin tikitin wasansa a dandalin The London 02 Arena a cikin minti biyu kacal.
Daga nan, Wizkid ya yi aiki da wasu fitattun taurarin mawaƙa a duniya, kamar Beyonce a waƙar "Brown Skin Girl" da Justin Bieber a waƙar "Essence" wacce mawaƙiya ƴar Nijeriya, Tems ta fito a cikinta.
Wizkid ya ce waƙoƙin mashahuran mawaƙa kamar King Sunny Ade da Fela Kuti na Nijeriya da kuma Sarkin waƙar Rege, Bob Marley sun ja hankalinsa matuƙa.
Bakandamiyarsa suna da yawa: Joro da Ojuelegba da Tease Me , da Pakurumo, da Sweet Love, da Caro da kuma Ginger da sauransu.
Wizkid yana alfahari da waƙoƙinsa a matsayin wani gaurayen waƙoƙi gwanin sha'awa: Afrobeat, da R&B da dancehill da kuma reggae.
Wizkid yana da Kyaututtuka da ya lashe aƙalla 40, da suka haɗa da kyautar Grammy a kan Waƙar Bidiyo da ta fi kowacce a matsayin mawaƙin da ya jagoranci waƙa a waƙar "Brown Skin Girl" ta Beyonce a 2021 da kuma kyautar BET a 2017.
Wizkid yana cajin tsakanin dala 800,000 zuwa dala miliyan ɗaya. Shi ne mahaifin yara huɗu da mata daban daban guda uku.
A faɗin Afrika, Wizkid ya yi aiki da Diamond Platnumz na Tanzania, da DJ Maphorisa na Afrika ta Kudu da kuma mawaƙan Nijeriya da ɗan dama da suka haɗa da mawaƙi Burna Boy da kuma sarauniya Afrobeat, Tiwa Savage a bisa ga misali.