Whitney Houston ta rasu tana da shekara 48 a duniya. Hoto: Getty Images      

A daidai lokacin da duniya ke bikin watan tuna gudunmuwar 'yan Afrika ga Amurka a watan Fabrairu, a ranar Alhamis mawakan duniya suka tuna mawakiya Whitney Houston, wadda ta fitar da kundin wakokinta na farko wanda ya samu darajar platinum - albam da aka sayar da sama da kwafi miliyan 1- mai suna 'You Give Good Love's kimanin shekara 39 da suka gabata. ( 22 ga Fabrairun 1985).

Whitney Houston ta mutu a shekara 12 da suka gabata a cikin ruwa a otel din Beverly Hills, kamar yadda rahoton coroners ya bayyana.

Ana tunawa da albam din ‘You Give Good Love’ ne domin shi ne ya daukaka mawakiyar ta zama fitacciyar mawakiya, sannan ta zama ta farko a cikin jerin bakaken mawakan na Amurka.

Wakar ta kuma shiga cikin gasar wakoki bangaren R $B a Gasar Grammys karo na 28 a shekarar 1986.

Mawakiya Whitney Houston ta lashe Grammy sau shida. Hoto: Getty Images

Many artists say the singer remains one of their greatest musical influences.

Mawaka da dama suna ganin mawakiyar tana cikin fitattun mawaka da suka kawo sauyi a masana'antar waka.

"Ita ce gwarzuwar mawakiya da na tsinkaya a rayuwata," inji wani masoyinta mai suna @medicboyc a shafin X.

Ana kuma tuna ta da wakar ta da ta yi, wadda ta yi shuhura sosai mai suna "Greatest Love of All" wanda asali mawakiyar Afirka George Benson ta yi.

Ana bayyana baitocin farko na wakar, inda take cewa: "Na yi amannar cewa yara su ne manyan gobe. Yana da kyau a ilimantar da su da sosai, sannan a musu jagora," a matsayin baitoci masu ilimantarwa, musamman yanayin lokacin da ake ciki yanzu da ake yawan kashe yara a yake-yaken da suke wakana a duniya.

Ana yabon Whitney Houston da yin amfani da baitoci masu ilimantarwa a wakokinta. Hoto: Getty Images

Whitney ta sadaukar da wakar ce ga kananan yara a fadin duniya, sannan tana ba da shawarar manya su rika karfafa gwiwarsu. Haka kuma a cikin wakar ta bayyana yaran a matsayin manyan gobe.

A bara, fitattun mawakan Amurka irin su Ariana Grande da Beyonce da Mariah Carey sun ce wakokinta suna cigaba da karfafa musu gwiwarsu.

Ariana Grande ta karrama Houston a taron kalankuwar da ta shirya, inda ta kwaikwayi wasu wakokinta, sannan daga bisani ta wallafa a shafinta na X cewa, "Ina farin cikin kwaikwayonta da na yi domin girmama babbar tauraruwata."

Beyonce ta ce, "Na dade ina kaunar zama kamar ta. Gwarzuwa ce ta daban."

Fitacciyar mawakiyar Afirka ta Kudu Belinda Davids ce ta aika da sakon jaje mafi daukar hankali, inda ta sadaukar tarukan kalankuwar da ta shirya kacokam ga mamaciyar.

TRT Afrika