Daga Pauline Odhiambo
Martin wanda ake kira da 'Safro Fades' Safari, ba irin wanzamin da ka saba gani ba ne.
Maimakon amfani da aska da almakashi, sai yake amfani da wuƙaƙe da shebur da guduma wajen yi wa mutane aski.
Mutane da ke kai kawo a kan titunan babban birnin Kenya, Nairobi na yawan tsayawa su kalli yadda Safari ke yi wa abokan cinikinsa aski.
Su kuma abokan cinikin nasa kan zauna ƙyam su miƙa wuta su bari Safari ya dinga bin salo-salo wajen amfani da shebur da sauran abubuwa masu hatsari a kusa da su.
Wani ƙirƙirarren salo
Wannan ƙirƙirarren salo na Safari ya jawo masa yin suna da ɗaukaka sosai.
Kuma in dai har ya yi wa mutum aski, to za a ga ya fito fes babu ko ɗigon gashi a tare da shi.
Safari ya samu lambar yabo ta wanda ya fi kowa iya wallafa abubuwa masu jan hankali a shafukan sada zumunta a Gasar Grammy ta 2023 ta wanzamai.
Ya shaida wa TRT Afrika cewa "ban halarci bikin ba da kyaututtukan ba saboda ban taɓa tunanin zan yi nasara ba."
'Ba-zata'
"An zaɓe ni ne tare da fitattun mutane da dama da kuma wanzamai waɗanda sun yi tafiya tafiye-tafiye sosai. Don haka nasarata ta ba ni mamaki sosai," ya ƙara da cewa.
Wanzami mai shekara 24 ɗan asalin ƙasar Rwanda ne, wanda ya koma Nairobi a ƙarshen shekarar 2023.
"Komawata Nairobi wata huɗu da suka wuce wani tsari ne. Na san cewa birnin zai taimaka wa sana'ata ta wanzanci mai sabon salo," in ji Safari, yana mai cewa kuma "kwalliya ta biya kudin sabulu.
An kalli wani bidiyonsa sau miliyan 95 a shafinsa na Instagram (safro_fades), wanda ke da mabiya 230,000.
Passion
Safari, ya bar karatunsa na digiri a fannin kasuwanci a wata jami'a a Rwanda, saboda ƙudurinsa na son ya ƙware a sana'ar wanzanci.
A watan Disamban 2022 ya wallafa bidiyonsa na farko yana nuna sabon salon wanzancinsa. A cikin bidiyon wanda ya watsu kamar wutar daji, ya yi amfani da guduma wajen yi wa mutane aski.
Safari ya ce bidiyon ya taimaka masa wajen samun ƙrin mabiya a Instagram daga 2,000 zuwa 100,000 a cikin ƙasa da sati uku.
"Ina so na zama na daban a matsayin wanzami," ya ce, yana mai bayyana cewa yana karɓar daga dala 45 zuwa 60 a duk askin mutum ɗaya.
Alkalin gasa
A shekarar 2023, an karrama shi a matsayin alkali a wata gasar wanzamai a Kamaru.
Safari ya ce: "Samun abokan hulɗar da za su yarda cewa ba za a samu matsala ba wajen yi musu aski shi ne babbar matsalae da nake fuskanta a sana'ata, ganin irin kayan da nake amfani da su."
Ya ƙara da cewa dole sai da ya dinga yi wa wasu aski kyauta a karon farko don su gamsu cewa ba za a samu matsala ba.
Safari na faran ƙirƙirar taron wanzamai na ƙasa da ƙasa don nuna wa duniya irin basirarsa.
Halartar tarukan horarwa
"Na yi amanna manyan taruka za su zame wa wanzamai masu basira wuraren tallata kansu ga duniya," ya faɗa.
Sannan kuma Safari na son ya samar da taruka na horarwa ga mutanen da ke son su ƙware wajen yin aski da irin salonsa.