Tyla ta kira lambar yabo ta  MTV a fannin waƙoƙin Afrobeat da ta 'musamman sannan mai ɗaci'

Tyla ta kira lambar yabo ta  MTV a fannin waƙoƙin Afrobeat da ta 'musamman sannan mai ɗaci'

Mawaƙiya Tlya ta soki  ''haɗa dukka mawaƙan Afirka ƙarkashin salon Afrobeats.''
Hoton Tyla ɗauƙe da lambar yabon da ta samu a fanni salon wakoƙi na Afrobeats na MTV Video Music Awards na 2024 a Elmont, New York  a wakar mai suna 'water'  / Hoto: Reuters   

Mawaƙiyar Afirka ta Kudu Tyla ta lashe lambar yabo ta Afrobeats na MTV video music awards da waƙarta mai suna 'water' a ranar Laraba.

Ƙyautar ''babba ce ga Afirka a wannan lokaci'', a cewar Tyla yayin da ta ƙarba ƙyautar.

''Tasirin da wakar ''Water'' ta yi a duniya ya tabbatar da cewa wakoƙin Afirka na tafiya da na salon zamani,'' in ji ta cikin yabo.

"Wannan tamkar na musamman ne sai dai mai ɗaci ne, saboda na san akwai yiwuwar haɗa kan dukka mawaƙan Afirka ƙarkashin salon Afrobeats.''

''Waƙoƙin Afirka suna da faɗi da banbanci - ya wuce iya Afribeats kadai,'' in ji Tyla.

Gagarumin nasarar Taylor Swift

Fitaccen mawaƙiyar Amurka Taylor Swift ta lashe ƙyaututtuka bakwai, inda ta yi ɗaiɗai da Beyonce a matsayin waɗanda suka samun karramawa a tarihin shirin na VMA a tsawon shekaru 40.

Swift ta kuma godewa magoya bayanta da suka kaɗa kuri'ar karramawa ta a shirin na VMA kazalika ta buƙace su da su kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar Amurka da ke tafe.

Mawaƙiyar ta kuma bayyana goyon bayanta ga 'yar jami'yyar Democrat Kamala Harris a wani sakon da ta wallafa a Instagram ranar Talata, amma ba ta ambaci sunan 'yar takarar ba a ranar Laraba.

Tun daga shekarar 1984 aka fara gabatar da shirin ba da lambar yabo na MTV kuma ya yi fice wajen kafa tarihi.

TRT Afrika