Matasan mawaƙan Afirka mata masu hasakwa Tyla da Ayra Starr

Tyla ta Afirka ta Kudu tana da shekaru 22 sannan Ayra Starr ta Nijeriya na da shekaru 21. Matan biyu sun sami manyan nasarori a shekarunsu na ƙuruciya.

Tyla ita ce mawaƙiyar Afirka mafi ƙaramcin shekaru da ta taɓa samun lambar yabo ta Grammy, inda ta taka matakin da manyan mawaƙa da suka taɓa karɓar kyautar a Afirka irin su Miriam Makeba ta Afirka ta Kudu da Angelique Kidjo ta Benin da Wizkid na Nijeriya da Burna Boy, da sauransu.

Waƙar Tyla mai suna "Water", wacce aka kalle ta sau sama da miliyan 600 a manhajar Spotify da kuma sama da miliyan 170 a YouTube, ta doke Burna Boy da Davido a Gasar Grammy ta 2024 a matsayin wakar da ta fi kowacce a Afirka. An ba ta kambin a watan Fabrairu.

Waƙarta ai taken "Water" ta kuma sake zama ta farko daga wani mawaƙin Afirka ta Kudu da aka ɗora a jerin Billboard Hot 100 tun bayan waƙar Hugh Masekela mai taken "Grazing in the Grass" ta shekarar 1968.

#MLZ89 : The 2024 Met Gala Celebrating "Sleeping Beauties: Reawakening Fashion" - Arrivals

'Sarauniyar popiano'

Ana kiran Tyla da suna 'Sarauniyar popiano'.

Yanzu kuma bari mu koma kan tauraruwa Ayra Starr.

An kuma zabi 'yar Nijeriyar a matakin Mafi kyawun Kyautar Wakokin Afirka a Gasar Grammys ta 2024, sai dai takwararta Tyla ce ta yi nasarar lashe kambin.

Ayra ta samu aƙalla kambi biyu da suka haɗa da Mace mawaƙiya da ta fi kowacce a 2023, ind ata doke takwarorinta biyu Tiwa Savage da Simi.

Ayra Starr: An haife ta Jamhuriyar Benin. Photo : Ayra Starr Instagram

Waƙa ɗaya da ta jawo mata nasara

Waƙarta ta "Rush" ta jawo mata ɗumbin nasarori.

An saurari waƙar sau aƙalla miliyan 358 a manhajar Spotify, sannan an kalle ta sau miliyan 340 a YouTube.

To wai ma su waye waɗannan matasan mawaƙan biyu na Afirka?

An haifi Tyla ranar 30 ga Janairun 2020 a birnin Johanneburg na Afirka ta Kudu. Asalinta ya haɗa da Indiya da Zulu da kuma ƙasar Ireland.

A wata hirarta da mujallar "Metal Magazine", ta ce tun tana ƙarama ba ta da burin da ya wuce ta zama mawaƙiya. / Photo: Getty Images

'Na daɗe da burin son zama mawaƙiya'

Sunanta na yanka Tyla Laura Seethal, kuma ita ce ƴa ta uku a cikin su biyar da iyayensu suka haifa.

Ta yi karatun sakandarenta a Edenglen High School a Johannesburg, daga can ta wuce jami'a don karatun digiri a fannin injiniya, amma ba ta kammala ba ta daina inda ta ci gaba da fafutukar zama mawaƙiya.

A wata hirarta da mujallar "Metal Magazine", ta ce tun tana ƙarama ba ta da burin da ya wuce ta zama mawaƙiya.

Takan ce "Tun a lokacin da na fara iya faɗar 'mawaƙiya', to abin da nakan gaya wa mutane cewa ina son zama kenan."

Ayra Starr: An haife ta Jamhuriyar Benin

Ayra Starr: An haife ta Jamhuriyar Benin

Tyla kan ce takenta shi ne: "A yayin da mutane ke bacci, ka yi ta aiki, za ka girbe sakamako mai kyau."

Tana da mabiya miliyan 15.4 a Tiktok da Instagram da Facebook da kuma X.

A yanzu kuma, bari mu koma kan Ayra Starr.

An haifi 'yar Nijeriya ne a garin Cotonou na kasar Benin a ranar 14 ga watan Yunin 2002 a cikin iyali mai 'ya'ya hudu. Sunanta na yanka Oyinkansola Sarah.

Zuri'ar fasihai

Daga baya dangin Ayra suka koma garuruwan Legas da Abuja a Nijeriya.

A cikin wata hira da aka wallafa a shafin intanet na Cibiyar Bayar da Rahoton Bincike ta Duniya a cikin Mayu 2023, ta ce ɗaya daga cikin 'yan'uwanta daraktan ɗaukar bidiyo ne, ɗayan kuma marubuci ne, kuma 'yar'uwarta abar koyi ce.

A cewar Ayra, malamin lissafin nata ne ya ƙarfafa mata gwiwa ta ci gaba da sana’ar waƙa, kuma a shekarar 2021 Mavin Records, wanda Don Jazzy na Nijeriya ya kafa, ya sanya mata hannu.

Mawaƙiyar ta Afrobeats ta yi digirin farko a fannin kimiyyar siyasa daga Jami'ar Benin ta Les Cours Sonou.

Ayra na da kusan mabiya miliyan 14 a kan duka shafukanta na sada zumunta.

TRT Afrika