Tyla (Daga hagu) da Ayra ne mawakan Afirka da suka fi yawan masu saurare a kan manhajar Spotify. Hoto: Others

Daga Charles Mgbolu

Magoya baya da masu sauraren wake-wake na shaida salon gogayya tsakanin shahararriyar mawakiyar Nijeriya Ayra Starr da mawakiyar da ta lashe Grammy 'yar Afirka ta Kudu Tyla, a lokacin da da dukkan su ke ci gaba da daukaka a masana'antar wake a Afirka da ma wajen nahiyar.

A yanzu Aytar ce mawakiyar Afirka ta biyu mafi yawan masu sauraro a spotify, inda tale da sama da mabiya miliyan 31 a kowanne wata a manhajar

A kowanne wata Ayra na samun masu sauraro 31,056,219 kamar yadda yake a watan mayu, tana bayan Tyla wadda ta kasance a kan gaba da masu sauraro 31,931,535 a kowanne wata, kamar yadda ita ma alkaluman watan Mayu suka nuna.

A farkon wannan watan na Mayu, Ayra ta haura wakar 'Calm Down' ta Rema dan Nijeriya, wanda ya zuwa 29 ga Mayu ke da yawan masu sauraro 24,551,231.

Yawan alkaluman masu sauraro

Ya zuwa yanzu, Tyla da Ayra ne mawakan Afirka biyu da ke da miliyoyin magoya baya, inda suka bar sauran abokansu a baya, kamar yadda alkaluma suka nuna.

Burna Boy (Nijeriya), wanda shi ma na daya daga mawakan Afirka da ake yawan saurare, na da mabiya rabin manyan sarauniyoyi inda yake da 15,583 a kowanne wata.

Tiwa Savage (Nijeriya), wadda a yanzu ke sahun mawakan da suka fi yin shuhura musamman a bangaren kida wakar afrobeat, na da masu sauraro miliyan 2,770,411.

Magoya baya a yanzu na tururuwa ga Ayra Star a yayinda masu sauraren ta ke ta kara yawa cikin sauri, musamman a lokacin da take shirin sakn rukunin wakokinta na ‘’The Year I Turned 21’’ a ranar 31 ga Mayu.

Tasowar Ayra

Tun bayan shigar ta kasuwancin waka a 2021, Ayra Starr ta zamo daya daga cikin manya kuma mashahuran mawakan Afirka da suka fito daga Nijeriya.

A 2023, wakarta ta 'Rush' da ta tsaya takara a Grammy ta samar masa da shaidar 'Diamond' a Faransa inda ta kuma zama bidiyon da aka fi kallo daga mawakiya 'yar Nijeriya a 2023.

A baya-bayan nan Ayra Starr ta shiga gasar '2024 BET Awards', ciki har da rukunin 'Sabuwar Mawakiyar da ta fi kowacce' da 'Mawakiyar Afirka da ta fi kowacce'.

Ayra ta lashe akalla kambi biyu, ciki har da Mawakiya Mace Mafi Kwarewa a 2023, inda ta doke irin su Tiwa Savage da Simi.

Tyla da ke kan gaba

Amma duk da yawan amsu suararo da ke daduwa, shi za ta iya kamo Tyla?

A nan ne masana ke tafka muhawara, a yayinda babu wani abu tabbatacce.

Tyla, mafi karanci shekaru a tsakanin mawakan Afirka da suka taba lashe gasar Grammy, har yanzu na girma da kara karfi.

Rukunin wakokinta da aka saki a watan maris din 2024, sun zama babbar nasara da jagora ga smaun dimbin masu sauraro, wanda suka sanya ta zama a sahun gaba.

Wakarta ta 'Water' da ta lashe kambin Grammy na cikin wannan rukunin wakokin, kuma a spotify kadai ta samu masau sauraro sama da miliyan 600 da masu kallo a YouTube sama da miliyan 170.

Wannan lamari ne na 'in ba ka iyawa ba ni waje', kuma masu kaunar wakoki ba za su je ko'ina ba.

TRT Afrika