Tauraron mawaƙin Afropop na ƙasar Ghana Stoneboy ya zama mawaƙin da ya fi samun nasara wajen lashe kyautar lambobin yabo a taron karrama mawaƙa na shekara-shekara wato 'Ghana music Awards' karo na 25 da aka yi ƙasar.
Stoneboy ya lashe lambobin yabo har guda shida, ciki har da ta gwarzon shekara wato 'Artiste of the Year' da marubucin waƙa ta shekara 'Songwriter of the Year' da mawaƙin da ya fi haɗaka da sauran mawaƙan da kasashen waje 'Best International Collaboratio' da kuma Best Reggae/Dancehall Artiste of the Year.'
Mawaƙa da dama ciki har da King Promise da Kuami Eugene da Nacee da Kofi Kinaata da sauransu suna daga cikin taurarun da bikin ya gwangwaje da lambobin yabo a bangarori daban-daban.
Stonebwoy ya wallafa saƙon godiya ga mabiyansa a shafinsa na X bayan manyan nasarorin da ya samu.
''Ga wadanda suka yarda da cewa ƙokari da jajircewata sun taka rawa wajen bayyana ainihin labarin da ya shafi rayuwarsu, wannan nasara taku ce,'' in ji sakon da ya rubuta a shafin X.
Mawaƙin afrobeats na Ghana, King Promise, wanda aka yi hasashe shi zai lashe kyautar lambar yabo ta gwarzon shekara, shi ma ya yi nasarar lashe lambobin yabo uku waɗanda suka haɗa da 'Afropop Song of the Year, da Afrobeat/Afropop Artiste of the Year da kuma waƙar da ta fi fice ta shekara.
Kazalika mawaƙin Nijeriya Davido shi ma ya zama zakara a taron bikin, inda ya lashe kyautar gwarzon mawaƙin Afirka na shekara.
Bikin taron wanda taurarun fina-finai Chris Atoh tare da Naa Ashorkor suka shirya, ya bai wa fitaccen mawaƙin nan Amakye Dede lambar yabo ta 'Lifetime Achievement.'
Sauran fitattun wadanda suka yi nasarar lashe lambobin yabon sun hada da Amerado, wanda ya lashe kyautar Wakar Highlife ta Shekara, da Kwesi Amewuga wanda ya lashe kyautar gwarzon mawaƙin bana.
An karrama waƙar 'Y'ahite Remix' wanda King Paluta tare da Kuami Eugene suka rera da lambar yabo ta wakar Hip-hop da ta fi fice yayin da yabo ta 'you are Great' da Kofi Karikari tare da Eternity ta samu lambar yabo ta mawaƙan da suka fi zaƙin murya ta bana.
An baiwa Queendalyn Yurglee lambar yabo a muryar mata mafi dadi a waƙarta ta 'Hold My Hands, yayin da waar Otan daga tauraron mawaƙi Sarkodie ta lashe lambar yabo ta waƙar da ta fice a fannin hip-hop.