Hagu zuwa dama: Ayoub Elaid, Kamal Lazraq, Abdellatif Masstour da suka yi nasara a kyuatr jury da fin din "Hounds" Hoto: Getty Images 

Daga Charles Mgbolu

Bikin fina-finai na duniya na Marrakech na 2023 da aka yi a Maroko ya ƙare tare da ba da sanarwar waɗanda suka yi nasara a kan manyan lambobin yabo a bikin rufe bikin da aka yi a ƙarshen mako.

Kyauta ta farko, lambar yabo ta Etoile d'Or, an ba ta ne ga mai shirya fina-finai 'yar Maroko Asmae El Moudir saboda aikinta a fim din ‘’Mother of all the Lies."

Asmae El Moudir ce ta zo ta farko. Hoto: Getty Images 

Shirin fim ɗin yana ba da labarin wata mata ne da ke neman gaskiyar tarihin danginta.

An fara shi a bikin fina-finai na Cannes karo na 76, inda fim din El Moudir ya lashe kyautar mafi kyawun shiririn "Documentary" tare da mai shirya fina-finan Tunisiya Kaouther Ben Hania.

An kuma zaɓe shi a zaman shigarwar ƙasar Maroko don mafi kyawun Fim ɗin Duniya a Gasar karo ta 96th.

Bikin dai ya gudana ne a matsayin wata alama ta juriya dangane da mummunar girgizar kasar da ta afku a Maroko Hoto: Getty Images 

An ba da kyautar juri ga wanda ya zo na biyu da na uku, "Bye Bye Tiberius" ta daraktar Falasdinu Lina Soualem da kuma "Hounds" na daraktan Maroko Kamal Lazrak.

Daraktar nan 'yar kasar Faransa da Senegal Ramata-Toulaye Sy ta tafi da lambar yabo ta gwarzon darakta da fim dinta na Banel & Adama.

Ramata-Toulaye Sy (ta tsakiya), ta lashe kyautar mafi gwarzon darakta da fim ɗinta na "Banel & Adama" Hoto: Getty Images 

Asja Zara Lagumdzija ta lashe kyautar gwarzuwar jaruma a wani wasan kwaikwayon ƙasar Bosnia mai suna Excursion, wanda darakta Una Gunjak ya rubuta kuma ya ba da umarni, Doga Karakas kuma shi ne ya zama gwarzon jarumi da fim din Turkiyya Nehir Tuna.

An dai dauki bikin a matsayin wata alamar juriya a yayin da kasar Maroko ke kokarin shawo kan mummunar girgizar kasar da ta afku a yankunan tsaunukan da ke kewaye da birnin Marrakech a watan Satumba.

TRT Afrika