Davido ya yi dawowar da aka daɗe ana jira a wannan shekarar da kundin waƙoƙinsa mai taken Timeless/ Photo: Reuters

Daga Charles Mgbolu

Nau'o'in waƙoƙi daga yankunan Afrika ta Yamma da kudu sun samu kyakkyawan ci-gaba a matakin duniya, a shekarar 2023, amma nau'in Afrobeat fice inda aka samu nasarorin haɗin guiwar waƙa a Afrika da sauran ƙasashen duniya.

Mawaƙan Nijeriya, musamman, sun jaddada tasirin waƙoƙinsu, ta hanyar kasance wa na farko a jerin zafafan waƙoƙi a Afrika da ma duniya, tsawon shekarar nan.

"Nijeriya wata cibiya ce ta ƙyanƙyashe masu baiwar waƙa, kuma muna matuƙar alfaharin nuna bambance bambance da Kuma shauƙi da masoya waƙoƙin Nijeriya ke da shi ta hanyar manhajar Wrapped," a cewar Phiona Okumu, shugaban manhajar Spotify a Afirka Kudu da Sahara.

"Manhajar Wrapped ta wannan shekarar wata sheda ce da ke nuna tasirin da waƙa ke da shi ta tattaro jama'a da kuma kai su kusa da al'ada da ɗabi'un Nijeriya."

Buƙatar sauraron waƙoƙin gida a Nijeriya na ci gaba da hauhawa a 2023, inda sauraron waƙoƙin ya ƙaru da kashi 284% gwanin sha'awa. Shi ma sauraron waƙoƙin mata mawaƙa a Nijeriya bisa matsakaicin ƙiyasi ya ƙaru da kashi 150%.

Rema

Waƙa mai taken Calm Down ta mawaƙi Divine Ikubor ɗan Shekaru Ashirin da Huɗu da haihuwa, wanda magoya baya suka sani da Rema, ta yi abin bam mamaki.

Tana cikin jerin Zafafan waƙoƙi Goma a aƙalla ƙasashen duniya da na Afrika guda 25, har da Amurka, da Birtaniya, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, da Switzerland, da Afrika ta Kudu, da Kenya da kuma Portugal.

Waƙar Rema mai taken Calm Down ita ce waƙar Afrobeat da aka fi sauraro a manhajar Spotify a shekarar 2023.

Waƙar na cikin kundinsa na farko da aka naɗa a sutudiyo mai taken Rave & Roses (2022).

Ya shiga jerin zafafan waƙoƙi a faɗin ƙasashen Turai, ta zama ta ɗaya a cikin zafafan waƙoƙin guda 50 na ƙasar Belgium, da guda 40 na ƙasar Holland da kuma waƙoƙi guda 100 na ƙasar Holland.

A Birtaniyya, waƙar ta tiƙe a matsayi na Uku, sannan ta shafe makwanni 25 ba a jere ba tana fitowa a jerin zafafan waƙoƙi Goma na Birtaniyya.

Ta zama waƙa nau'in Afrobeat da aka fi sauraro a manhajar Spotify a shekarar 2023, kuma ta farko da ɗan Afirka ya rera da ta aka kallla sau biliyan ɗaya a manhajar.

Waƙar kuma ta kasance ta farko da ta shafe shekara ɗaya cir a jerin zafafan waƙoƙi Afrobeat na Billboard.

Asake

Ahmed Ololade, wanda aka fi sani da Asake, ya kafa tarihinsa da waƙarsa da ta yi shuhura mai take Lonely a saman kundinsa mai taken Work of Art da aka saka a watan Yuni. Ta zamo waƙa ta farko a tarihin Audiomack da waɗanda suka kallle ta suka zarce miliyan 100.

Ya samu gagarumar nasara, yayin da a wasansa, aka sayar da tikiti 20,000 a dandalin kaɗe kaɗe da raye raye na 02 Arena a London, a watan Agusta 2023.

A watan Nuwamba na 2023, an zaɓi Asake domin shiga takarar karɓar kyauta a karon farko, a kyautar Grammy ta shekara shekara jiƙo na 66th, da waƙarsa mai taken 'Amapiano' wacce Olamide ya fito a cikin ta.

A cewar manhajar Spotify Wrapped ta 2023, Asake na jawo ra'ayin jama'a a faɗin Nijeriya, da Ghana da kuma Togo, abin da ya ba shi kyautar Gwarzon Mawaƙin da aka fi sauraron waƙarsa a kowacce daga ƙasashen.

Ayra Starr

Oyinkansola Sarah Aderibigbe, wacce magoya baya suka sani da Ayra Starr, ita ce mawaƙiyar da aka fi sauraron waƙarta a 2023, in ji wasu alƙaluma daga manhajar Spotify, inda take da masu sauraron ta fiya da miliyan 12.

Ayra Starr ta samu shekara mai kyau, wadda a cikin ta, ta yi ta ɗaya, a jerin zafafan waƙoƙi a ƙasashe dayawa.

Nasararta a 2023 asali ta fara ne a 2022 da ta saki waƙarta mai taken 'Rush'. Ta kasance ta zo na ɗaya a jerin zafafan waƙoƙi a ƙasashe dayawa, har da Switzerland, da Ireland da kuma Birtaniyya, inda ta tiƙe a matsayin ta 24.

Waƙar har ila yau, ta bai wa Starr damar shiga takarar neman kyautar Gwarzon Mawaƙin Afrika, a Bukin Miƙa Kyaututtuka na Grammy na shekara shekara jiƙo na 66th.

Waƙar kuma ta zamar da Starr mawaƙiyar Africa mace mafi ƙarancin shekaru da waɗanda suka kalli waƙarta a bidiyo ɗaya tal a Youtube suka zarce miliyan 100, kuma wacce ta yi hakan a cikin watanni Biyar.

Burna Boy

Damini Ebunoluwa Ogulu, wanda aka fi sani da Burna Boy, shi ma wani jigon waƙa ne da ya fito daga Afrika yana da masu sauraron shi sama da miliyan 16, a cewar alƙaluman 2023 daga Spotify.

Burna Boy ya ci gaba da riƙe matsayinsa a fagen waƙoƙin Afrobeat inda ya gama shekarar a gaba gaba.

A 2023, Rolling Stone ya saka shi a matsayin lamba na 197 a cikin kundisa na jerin mawaƙa mafi shahara guda 200 na kowane lokaci.

Har illa yau, Burna Boy ya lashe kyautar Bet International Act a Bukin Kyaututtuka na BET na 2023, abin da ya zama lashe kyautarsa jiƙo na huɗu kenan a wannan rukunin.

Har wa yau, Burna Boy ya samu galaba a 2023 da ya zo na ɗaya, a Jerin zafafan waƙoƙin na Billboard na mawaƙan Afrobeat na Amurka na ƙarshen 2023, yayin da waƙar Rema ta sauka daga jerin a watan Oktoba, bayan ta kasance a matsayin ta ɗaya na tsawon kimanin makwanni 52.

Ta gama a matsayi na biyu a wannan rukunin a 2022 saboda haka dole ya samu sa'idar gama shekara a matsayi na ɗaya.

Davido

Tauraron waƙoƙin Afrobeat na Nijeriya Davido ya kasance ana damawa da shi kowacce shekara tare da waƙoƙi masu tashe, kuma bana ma ba ta sauya zani ba.

#LBP07 : BET awards 2023

Kundin waƙoƙinsa mai take Timeless ya kasance ɗaya daga cikin jerin kundaye 50 mafi shahara na Billboard a 2023.

Timeless Shi ne kundin waƙoƙin da Davido ya yi bayan ya ɗau wani lokaci ba ya waƙa, kuma ya ƙunshi mawaƙa irin su Drake (For All the Dogs), Metro Boomin (Spider-Man: Across the Spider-Verse, da kuma Cat’s Scarlet na Doja.

TRT Afrika