Daga Charles Mgbolu
Kamar salon kida na Afrobeats, shi ma salon kiɗan Amapiano ya yi tashe mai ban mamaki a shekarar 2023, inda ya yaɗu ya shahara kuma yana taimakawa mawaƙan da suka ƙware a salon isa saman jadawalin waƙe-waƙe.
Shahararren salon ya haɗa da salon jazz da na lounge, ya kuma samo asali daga Afirka ta Kudu a tsakiyar shekarun 2010.
Kamfanin Spotify ya saki taƙaitaccen bayani a kan yadda salon kiɗan ya ja zarensa a shekarar 2023, wanda ya bayyana yadda shaharar salon ta ƙru da kashi 101% idan aka kwatanta da bara.
Rahoton ya nuna cewa mafi yawan ƴan Afirka ta Kudu suna sauraron waƙoƙin da aka yi a ƙasar, inda aka fi jin waƙoƙin Mnike na Tyler ICU da Hamba Juba ta Lady Amar.
Sauran sun haɗa da waƙoƙin na Kabza De Small biyu na KOA II Kashi na Farko da The Konka Mixtape: Sweet & Dust da ma waƙoƙin Kabza De Small da DJ Maphorisa.
Tara daga cikin goma na fitattun wakokin da aka fi sauraro a Afirka ta Kudu na ‘yan Afirka ta Kudu ne, a cewar Spotify, inda aka samu babban bambanci daga shekaru biyu da suka gabata lokacin da waƙoƙin ƙasashen duniya suka mamaye jerin.
Shahararsu ta riga ta yadu a tsakanin mawaƙan Nijeriya irin su Asake, wanda aka fi sani bisa nasarar da waƙoƙinsa suka samu.
Mawaƙin Nijeriya da ke tashe a yanzu Rema ya ce yana matukar yin nazari kan bambancin wakokinsa don nuna sautin Amapiano.
Ya gaya wa Nandi Madiba na shirin Applesic Africa Now Radio cewa: ''Ina jin kamar in kunna sauti, musamman idan yana cikin Afirka. Ina ɗaukar lokacina don yin karatu. Ba na hanzarin shiga cikin salon; Ina ɗaukar lokacina don fahimtar abubuwa.''
Amapiano yana nuna babbar damar mamaye fannin waƙa har zuwa 2024, tare da haɗin gwiwa a cikin ayyukan da mawaƙan gida da na ƙasashen waje.