Kundin wakoki na uku na Asake mai suna, 'Lungu Boy', bai ba shi kunya ba, sakamakon kundin waƙoƙin mai ɗauke da waƙa 15 ya kafa tarihi a shafukan intanet daban-daban da ake sauraren waƙoƙi.
Sharararren mawaƙin nan na Nijeriya Wizkid da mawaƙan gambarar nan na Birtaniya Central Cee da Stormzy da shahararren mawaƙin nan na Amurka Travis Scott da mawaƙiyar nan ta ƙasar Brazil Ludmila na daga cikin waɗanda suka shiga cikin kundin waƙoƙin nasa.
Shafin Turntable wanda ke bayar da ƙididdiga game da waƙoƙi ya bayar da bayanai dangane da irin tarihin da kundin wakokin nasa mai kwana biyar ya kafa. Kundin waƙoƙin shi ne mafi girma da ya jawo jama'a a ranar farko da aka ƙaddamar da shi a manhajar sauraren waƙoƙi ta Spotify.
An saurari kundin sau miliyan 5.86 a Spotify a Nijeriya a ranar farko ta ƙaddamar da kundin. Wannan tarihin ya zarta wanda Davido ya kafa a baya da ya saki kundin waƙoƙin nasa na 'Timeless' wanda aka kalla sau miliyan 4.91.
'Lungu Boy' a halin yanzu shi ke da wannan kambu na waƙoƙin Nijeriya da aka fi saurara a kwana guda a faɗin duniya inda ya samu miliyan 9.2.
Waƙoƙin Nijeriya waɗanda ke kan gaba
Waƙa ta biyu da ke cikin kundin mai suna 'MMS' wadda Wizkid ke cikinta an saurare ta sau 870,577 a ranar farko na sakinta a Spotify a Nijeriya, wanda hakan ya sa ta kafa tarihin wuce wadda Wizkid ya saka ta IDK' feat. Zlatan mai 626,000.
Waƙar da Asake ya fitar ta baya-bayan nan ita ce ta farko a waƙoƙin Nijeriya a waƙoƙin Apple na Amurka, inda a baya waƙar Burna Boy ta 'I Told Them' da kuma ta Wizkid ta Timeless' su ne suka riƙe wurin.
Asake shi ne mawaƙin Nijeriya na farko da ya soma yin kundin waƙoƙi uku da suka zama na farko a manhajar sauraren waƙoƙi ta Apple Music bayan ya saki kundin waƙoƙi na 'Mr. Money With The Vibe' da kuma 'Work of Art'.
A halin yanzu 'Lungu Boy' na kan hanyarsa ta kafa tarihin mafi girma a mako guda a manhajar Spotify Nigeria wanda a halin yanzu kundin Davido na 'Timeless', ke da kambun inda aka kalla sau miliyan 14.4
Lungu a rana ta hudu an saurara sau miliyan 13.52/