Masu shirya bikin lambar yabo ta Gasar Academy Awards karo ta 96 (Oscars 2024) sun fitar da jerin sunayen wadanda aka zaba, inda fim din tarihin Amurka "Oppenheimer" ya sami mafi yawan wadanda aka zaba.
Fim din ya sami shiga gasar da matakai 13, sai kuma fim din "Poor Things," wanda ya sami shiga gasar da matakai 11.
Masu shirya fina-finai daga nahiyar Afrika su ma an fitar da sunayensu a fannoni daban-daban a shekarun baya.
An zaɓi fim ɗin Ugandan ‘Bobi Wine: The People's President' wanda Christopher Sharp da Moses Bwayo suka rubuta kuma suka ba da umarni a matsayin mafi kyawun fasalin Documentary.
An nuna fim din wanda ya shafi rayuwa da burin mawaƙin Uganda Bobi Wine, wanda ya zama ɗan siyasa a taron bikin fina-finai na Venice Film Festival karo na 79.
"Akwai matukar jin dadi da alfahari ganin wani fim na Uganda ya kai ga samun lambar yabo ta Academy, kyauta mafi girma da muhimmanci a duniya ... Na gode da wannan girmamawa!" Bobi Wine ya fada a shafin X.
Har ila yau, an zabi fim din kasar Tunusiya Four Daughters, a cikin mafi kyawun Documentary.
Kaouther Ben Hania ce ta rubuta kuma ta ba da umarni inda ta ba da labarin wata uwa ’yar Tunisiya wacce ta nemi ‘ya’yanta mata biyu da suka bata.
Fim ɗin ya shiga gasar Palme d'Or a bikin Fim na Cannes karo na 76, inda aka fara nuna shi a duniya a ranar 19 ga Mayun 2023.
An zaɓe shi a matsayin fim din da aka shigar gasar daga kasar Tunisiya a matsayin Mafi kyawun Fim na Duniya a Kyautar Academy Awards karo na na 96 kuma an zaɓe shi a matsayi Mafi kyawun shirin Documentary.
Fim ɗin 'Io Capitano' na ƙasar Senegal shi ne fim na uku da aka zaɓa don shiga gasar Oscar ta bana.
Lo Capitano ya ba da labarin balaguron ban sha'awa na wasu samari biyu, Seydou da Moussa, waɗanda suke kokarin shawo kan cikas daban-daban yayin tafiya daga Dakar zuwa Turai.
Mai shirya fina-finan Italiya Matteo Garrone ne ya rubuta shi kuma ya ba da umarni kuma ya fafata a bikin fina-finai na Venice na kasa da kasa karo na 80, inda ya lashe lambar yabo ta Silver Lion.
Haka nan an zaɓe shi a mafi kyawun Fim da Harshen kasar Waje a Gasar Golden Globe Awards karo ta 81 sannan aka zabe shi a matsayin Mafi kyawun Fim na Duniya a Gasar Academy Awards karo ta 96.
Gasar Academy Awards karo ta 96 za ta gudana ne a wani biki mai kayatarwa a Los Angeles a ranar 10 ga Maris.