Daga Emmanuel Onyango
Ma'aikacin gandun daji na Zimbabwe, Jealous Mpofu ne kungiyar bayar da taimako ta Tusk ta ba shi matsayin gwarzon shekara.
Mpofu ya lashe kambin '2023 Tusk Wildlife Ranger Award' saboda kokarinsa na kare karnukan dawa da ke Afirka, da ake kira karnuna masu fenti, a Dajin Kasa na Hwange -- daji mafi girma a kasar.
A makon nan zai tafi Ingila don karbar kambin tare da kuma kudi har dala dubu talatin da bakwai ($37,000).
Mpofu ne shugaban bindiddigin karnuna na Kungiyar 'Painted Dog Conservation' da ke bin diddigi tare da ganin inda karnukan daji suke a Dajin Kasa na Hwange.
Karnukan dawa
Shi ne ke da alhakin kawo rahoton inda karnuka suke a yankunan da ake rikici zuwa ga ofishin yaki da farautar dabbobin dawa, kuma yana jagorantar su zuwa ga kwance tarkunan da aka dana don kama karnukan, in ji kungiyar Tusk.
"A ko yaushe yana fara amsa kira game duk wata buakata da aka kawo game da karnukan, yana gaggawar daukar matakin hana su cutuwa," in ji Peter Blinston, daraktan zartarwa a cibiyar 'Painted Dog Conservation'.
Akalla akwai karnukan dawa 7,000 a dazukan nahiyar Afirka, kamar yadda kungiyar 'Painted Dog Conservation' ta bayyana.
An sha samun tashe-tashen hankula tsakanin namun daji da mutane a 'yan shekarun nan a kasar Zimbabwe.
Barazana ga namun dawa
Hukumar kula da gandun daji da rayuwar dabbobin dawa ta kasar ta ce sama da mutum 80 giwaye suka kashe a 2021 kawai, inda daruruwa suka samu raunuka bayan harin da wasu dabbobin irin su kada da kuraye suka kai musu.
Wani bincike da kungiyar 'Fauna and Flora Zimbabwe' (FAfloZIm) ta gudanar kan shugabannin jama'a da lauyoyi kwararru, ya bayyana masu farauta na jefa rayuwar namun dawa cikin hatsari.
Rahoton shekarar 2021 da Kungiyar Kula da Namun DAawa ta Duniya (WWF) da Hukumar Kula da Muhalli ta Dajalisar Dinkin Duniya (UNEP) suka fitar ya yi gargadi kan rikici da namun dawa wand aya zama babbar barazana ga dorewar su a ban kasa.
Amma tare da kokarin kungiyoyin da sauran jama'a irin su Mpofu, kwararru na fadin cewa ana sa ran za a dinga kubutar da rayuwar dabbobin na dawa.