Mawaƙin nan ɗan Amurka kuma mai rubuta waƙa, Steveland Morris, da aka fi sani da Stevie Wonder ya ce ya cika ɗaya daga burikansa na rayuwa, bayan an ba shi shaidar zama ɗan Ghana.
Mawaƙin ya yi bikin cikarsa shekara 74 a duniya ranar Litinin a babban birnin Ghana, Accra tare da iyalansa, inda Shugaba Nana Akufo-Addo ya gabatar masa da takardun zamansa sabon ɗan ƙasa.
A yanzu ya kasance ɗan ƙasashe biyu, Amurka da Ghana.
"Ina ji kamar nan ne asalina. Ina jin Ghana a jikina, ina jin cewa tushena a nan yake, kuma nan ne mafarin tarihina," ya ce.
Tun 2019 Ghana ta fara wani yunƙuri a cikin shirinta mai suna "Year of Return", na gayyatar 'yan asalin Afirka da ke zaune a ƙasashen waje, wanda yake ƙarfafa gwiwar 'yan asalin nahiyar su "dawo gida".
Shugaba Akufo-Addo ya yaba wa Stevie Wonder saboda gudunmawarsa ga waƙa, da kuma sadaukarwarsa ga 'yan Afirka da suke ƙasashen waje, a cewar wata sanarwa daga Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Ghanan.
Ta ce mawaƙin "yana farin cikin a yanzu a ce masa ɗan Ghana."
"Abin da ya faru zai sa a ƙara samun haɗaka da musaya tsakanin Ghana da 'yan Afirka da ke ƙasashen waje," a cewar sanarwar.
Mawaƙin wanda ya taɓa lashe kyautar Grammy na ɗaya daga cikin mawaƙan da aka fi sayen waƙoƙinsu. Wonder ya kuma yi fafutukar mayar da ranar haihuwar Martin Luther King Jr a matsayin ranar hutu a Amurka a 1980.
A shekarar 2019 aka ƙaddamar da shirin Ghana na "Year of Return" wato Shekarar Komawa Gida, da ya sa Amurkawa da 'yan ƙasashen Turai 'yan asalin Afirka da dama suka ringa tururuwa zuwa Ghana don ziyarar ganin asalinsu.
An yi bikin ranar ne shekaru 400 bayan bayi baƙaƙe na farko daga Afrika sun isa Amurka.