Daga Charles Mgbolu
Watan Janairun 2024 ya kama cikin ba zata ga masu shirya fina-finai da dama a Nijeriya inda aka ga masu kallo na ta tururuwar sayen fina-finai a lokutan hutu.
Sabon fim din jaruma kuma mai shirya fina-finai a Nijeriya Funke Akindele mai suna 'A Tribe Called Judah', ya kafa tarihi bayan da ta sayar da kwafi na Naira biliyan 1.5 (dala miliyan $1.6) a cikin kwanaki 21.
Toyin Abraham, wata ita da ke shirya fina-finai a Nijeriya, ta kafa tarihi a karan kanta a yayin da ta saki shirin fim din ta mai suna Maika wanda a wata guda ta sayar da kwafi har na Naira miliyan 283,352,445 (dala dubu 315,000).
Sai dai kuma, nasarar da wadannan fina-finan ke samu na fuskantar barazana daga 'yan kwafa-sayar, wadanda kawai suke yada fina-finai a shafukan sada zumunta ba bisa ka'ida ba.
'Mafarki nake yi?
Toyin Abraham ta shaida wa 'yan jarida cewa ta fashe da kuka a lokacin da ta ga shirin fim dinta na Malaika a shafin sada zumunta.
"Na tambayi manajana. 'Mafarki nake yi? ya ce 'A'a', sai abin ya zama kamar rayuwata ta zo karshe kenan.
Hukumar UNESCO ta kiyasta cewa kaso 50 zuwa sama da 75 na kudaden da masu shirya fim ya kamata su samu na salwantuwa sakamakon 'yan kwafa-sayar.
Abraham ta kuma ce ta ga yadda kamar rayuwarta ke ƙarewa.
"Na tunkari wadannan shafuka na sada zumunta biyu inda aka yada fim di na, na roki wadanda suka kwafa suka yada, amma abin ya ci tura".
Ba Toyin Abraham ce kadai ke fuskantar wannan kalubale ba.
Babbar sata
Kungiyar Masu Gidajen Cinema ta Nijeriya (CEAN) ta bayyana cewa shirin fim din Funke Akindele na 'A Tribe Called Judah' ya fuskanci raguwar samun kasuwa da kaso 55 a tsakanin 12 da 18 ga Janairu 2024.
Wannan ya zo daidai da lokacin da labaran kafa tarihi suka karade kafafen yada labarai wanda hakan ya fargar da 'yan kwafa-sayar.
Nan da nan, wai aka samu adreshin yanar gizon kallon shirin fim din a shafuka da yawa, hakan ya sanya makusanta da abokai suka yi ta kira a kafafan sada zumunta suna sukar wannan aibu, suna kuma kira ga jama'a da su kalli fim din ta hanyoyi na halaliya.
Abraham ta ci gaba da cewa tabbacin masu kallo na za su samu wajen kallon fina-finan a shafukan sada zumunta ne yake kara wa mugun halinsu karfin gwiwa.
Ta ce "A shafukan sada zumunta, mutane na cewa ba za su je dakunan cinema kallon fim ba. Muna jiran samun link din da za mu kalla... wannan ya janyo min diamauta sosai."
Adireshin yanar gizo da ba sa bisa ka'ida
Don kubutar da shirin fim din Malaika daga mutuwa a hannun 'yan kwafa-sayar, Abraham da tawagarta sun yi kiran gaggawa ga kwararru kan shafukan sada zumunta, wanda suka dinga aikin lalata adireshin yanar gizon.
Ta ce "Mun lalata da dama daga irin wadannan adireshi na yanar gizo, har yanzu kwai wasu da yawa,"
Rundunar 'yan sandan jihar Legas sun yi baje-koli wasu mutum biyar da aka kama bisa zargin yada adireshin yanar gizon shfin da za a kalli fim din Malaika, in ji Abraha inda ta kara da cewa ita ba wadannan 'yan aiken ne suka dame ta ba.
"Ina son na san wa ya saka su yin hakan. Wadannan mutane sun kwafi shirim fim di na. Ta yaya hakan ta faru? Ina son na san wanda ke da alhakin aikata wannan aika-aikar."
Ta sha alwashin ita da kanta za ta dinga yaki da 'yan kwafa-sayar, tana mai cewa "Ba wai ga ni kadai ba, sai don amfanin duk masu shirya fim a Afirka."