Daga Brian Okoth
Mawaƙan DRC Fally Ipupa da Ferre Gola suna yin abubuwa da dama masu kama iri ɗaya. A shekara 46, Fally na cikin ruƙuni ɗaya da Gola mai shekaru 48.
Tauraron biyu sun taba aiki tare da fitaccen mawaƙin nan Koffi Olomide kuma sun taka rawa sosai a fagen nishaɗi a daban-daban a Afirka.
Da irin askin gashin kansu da gemunsu na 'yan gayu da kuma adon suturansu. Wanda bai san su ba zai ɗauka Fally da Gola 'yan'uwa ne a duniyar da mutane kaɗan suka san su.
Sun samu duniyarsu a yayin da suka shahara. Kuma ta haka muka ƙaunace su tare da yaba mu su— daidai kuma daban-daban.
A cikin wannan yanayi ne, masoya sun yin taho-mu-gama a duk lokacin da aka taso kan wanene a tsakaninsu ya fi wani ko kuma ya cancanci zama sarkin salon waƙoƙin Rhumba na wannan zamani.
Wannan muhawarar ba ta taba ƙarewar nasara ko akasin hakan ba, domin mawaƙan Fally da Gola sun ƙware kan abin da suke yi.
Wannan shi ne labarin tauraron mawaƙa biyu na DRC a wannan zamanin.
Mawaƙi ɗaya
Za mu fara ne da Gola - ba don wani dalili ba.
An haife shi a ranar 3 ga watan Maris na 1976 a Kinshasa babban birnin DRC. Sunan da aka fi sanin sa da shi a fagen nishaɗi shi ne Hervé NGola Bataringe
A farkon shekarun 1990 ne sha'awar son waƙa da Gola ke yi ta ƙaru sosai, a lokacin yana matashi.
A tsakiyar shekarun 1990, mawaƙin Kongo kuma furodusa Werrason ya sanya Gola a cikin ƙungiyar Wenge Musica soukous. a lokacin yana ɗan kimanin shekara 18 a lokacin.
Ƙungiyar Wenge Musica ta raɓe a 1997, amma Gola ya bi Werrason zuwa wata sabuwar ƙungiyarsa.
Gola ya zauna tare da ƙungiyar har tsawon shekaru bakwai.
A ƙoƙarin haɓaka aikinsa, Gola ya haɗa kai tare da abokansa guda biyu don ƙirƙirar wata sabuwar ƙungiya a shekarar 2004.
Ko da ya ke , ƙungiyar ba ta wani ɗaure ba, bayan ne Gola ya samu gurɓin shiga tawagar mawaƙan Koffi Olomide's ''Quartier Latin International'', wanda ya wanzu tun daga shekarar 1986.
A shekara ta 2006, Gola ya tsunduma salon yin waƙa shi kadai, inda rahotanni suka bayyana cewa shi da Olomide sun yi hannu-riga.
A yanzu, mawaƙin mai shekaru 48 da ya lashe lambar yabo yana da tarin waƙoƙin da suka yi fice kamar su "Mea Culpa", "Vita Imana", "Visas", da "Jugement", da dai sauransu.
A shafin Facebook, da Instagram, da X, da kuma TikTok, yana da mabiya miliyan 5.3. Sannan mawakin yana da yara da yawa.
Mai ba da umarni
Yanzu, bari mu koma kan Fally Ipupa.
An haife shi a ranar 14 ga watan Disamba na 1977 a Kinshasa. Sunansa da aka fi saninsa a fagen nishaɗi shi ne Fally Ipupa N'simba.
Mawaƙin, wanda ya taso a zuru'ar mabiya addinin Katolika, a bayan ya bayyana cewa kasancewarsa a cikin mawaƙan coci ne ya taimaka samun kwarin gwiwa iya fuskantar tarin jama'a.
A 1997, Fally ya fara soma sana'arsa ta yin waƙa ntare da ƙungiyar Talent Latent wadda ta samo asali daga Kinshasa.
Bayan shekara biyu, a soma waka tare da ƙungiyar Koffi Olomide ta Quartier Latin International.
Olomide ya ji daɗin basirar aikin Fally, wanda ya kai ga ƙungiyar ta fitar da manyan waƙoƙin da suka shahara kamar "Force de frappe".
Domin sakawa Fally bisa ga gudummawar da ya bayar, Olomide ya kara masa girma zuwa mai ba da umarni a ƙungiyar, a shekarar 2006 - bayan shekaru bakwai tare da Quartier Latin - Fally ya zaɓi aikin sana'arsa shi kadai.
A kunɗin waƙoƙinsa na farko mai suna "Droit Chemin" ya sayar da fiye da kwafi 100,000, sannan ya gabatar da takardun shaidar Fally ga duniya
A yanzu haka, mawaƙin mai shekaru 46 ya samu nasara da dama, kuma yana da tarin mabiya, wasu daga cikin manyan waƙoƙinsa da suka yi fice sun haɗa da "Associé" da "Mayday", da "Amore" da kuma "Ecole."
A shafin Facebook, da Instagram, da X, da kuma TikTok, Fally ya haɗa jimilar mabiya miliyan 19.6.