Wani lamari wanda ya yi barazana ga rayuwar Alex Nderitu ya jawo ya rubuta litattafai goma a shekara. / Hoto: Alex Nderitu

Stephen King, fitaccen marubucin nan Ba’amurke wanda yana daga cikin wadanda suka fi sayar da littattafansu ya taɓa shaida cewa a duk rana yana rubuta aƙalla kalmomi 2,000, ko a ranar aiki ko kuma ranar ranar hutu.

A 2023, marubucin nan ɗan Kenya kuma mai rubuta rubutacciyar waƙa, Alexander Nderitu ya kafa tarihi inda ya wallafa littattafai mafi yawa a cikin shekara guda.

Nasarar da mutumin ɗan shekara 45 ya samu, ta samo asali ne bayan ya shafe sama da shekara 20 yana ƙoƙarin gogewa a harkar rubutu. Sai dai bai san yana da irin baiwar ba sai da wani abu ya faru wanda hakan ya buɗe masa hanya.

Rubutun da bai kammalu ba

Wani hali da Alex ya shiga a 2021 na barazana ga rayuwarsa shi ja yawo ya wallafa littafai goma a shekara guda.

"Cutar korona ta kwantar da ni, kuma abin mamaki sai aka kai ni asibitin da aka haife ni. Sakamakon yadda aka kwantar da ni a kan gadon asibitin nan sai na shiga wani hali saboda na ɗauka zan mutu ne," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"Abin da kawai nake tunani a lokacin shi ne rubutun da ban kammala ba waɗanda na shafe kusan shekara 20 ina aiki a kansu. Hakan ne ya sa na yi alƙawarin wallafa rubuce-rubucen da na yi dama idan na samu sauƙi."

Litattafai 10 da Alex ya wallafa a 2023 rubuce-rubuce ne da ya shafe sama da shekara 20 yana yi. / Hoto: Nderitu

Ba wai Alex ya rayu kaɗai don ya bayar da labarin cutar da ya yi fama da ita kaɗai ba, ya ƙara samun ci gaba a harkarsa ta rubutu.

Kamar wasa, Alex ya samu kansa inda ya rinƙa yin aiki ɗaya bayan ɗaya inda yake kammala rubuce-rubucen da ya soma tsawon lokaci amma ba zai taɓa yin nasara ba ko ginawa akan ayyukan da ya riga ya sami yabo.

"Hannah and the Angel wani gajeren wasa ne wanda ya lashe kyauta a 2004. Na yi tunanin zan iya haɗawa da shi na mayar da shi littafi wanda na yi hakan a 2023," in ji Alex.

Wani littafinsa kuma shi ne : The Good, The Bad, and the Ugly, wanda doguwar bita ce mai muhimmanci wadda ta dogara a kan labarin mai suna iri ɗaya da aka fara bugawa a cikin 2014.

"Wannan rubutun shi ne rubutuna wanda aka fi karantawa, inda na tambaya me ya sa babu wani wasa game da ɗaya daga cikin wadda ta ci kyautar Nobel kan muhalli ƴan Kenya wato Wangari Maathai," kamar yadda Alex ya shaida wa TRT Afrika.

"Idan Afirka ta Kudu za ta iya samun Winnie Mandela ta ɓangaren waƙa, Nijeriya tana da Fela Kuti, hakan na nufin Maathai, mace ta farki a Gabashi da Tsakiyar Afirka da aka taɓa ba ta digirin dakta, ya kamata a ce akwai littafi ɗaya game da rayuwata.

Ya ƙosa ya ga littafi a game da Maathai wanda ya rubuta da kansa a 2021.

Alex ya samu kyaututtuka da dama waɗanda daga cikinsu akwai kyauta daga Theatre Company a 2004. / Hoto: Nderitu

Rayuwa ta haɗu da almara

Maganar bishiyoyi, wanda labari ne da aja rubuta dangane da rayuwar Maathai, ya an yi shi babi har takwas, a maimakon uku da aka saba yi.

Alex wanda ya shafe shekara uku kafin ya kammala littafin, ya zaɓi ya yi rubutun littafin da tsawo "sakamakon ta yi rayuwa mai kyau".

Maathai wadda ta lashe kyautar Nobel, haka kuma wadda ta ƙirƙiro Green Belt Movement da kuma UNEP Million Tree, inda ta assasa wani yunƙuri na shuka bishiyoyi a Kenya.

Tun da farko an saki littafin Talking of Trees a 2021 bayan an jingine shirin da ake yi na yin fim a kan littafin sakamakon annobar korona.

"Duk da cewa littafin The Talking of Trees an yi shi ne dangane da abubuwan da suka faru a gaske, amma yana da kyau a san cewa almara ce. A wasa na, President (Daniel Toroitich arap) Moi ya yi waƙa bayan ya ci zaɓe," kamar yadda Alex ya yi ƙarin bayani.

"Wasan bai ƙare da mutuwar Maathai ba; sai dai kawai ya bayyana irin tsantsar nasar da ta samu."

Shiga kafafen sada zumunta

Alex ya rubuta littafinsa na farko, When the Whirlwind Passes, a 2001. Wannan littafin da ya yi yana kan yanar gizo ne kaɗai inda sai a 2022 aka yi shi na takarda.

Alex Nderitu da 'yan uwansa marubuta a bikin littattafi na 2023. / Hoto: Nderitu

"Ina so na zama mai rubutun ban mamaki irin Fredrick Forsyth ko kuma Jeffrey Archer. Sai dai zuwa farkon shekarun 2000, akwai shahararrun marubuta waɗanda ba su wuce biyar ba, inda dukansu suka ƙware wurin wallafa littattafan makaranta," in ji Alex wanda ya karanta fasahar sadarwa a tattaunawarsa da TRT Afrika.

"Aikina a fasahar sadarwa ya sa na gano cewa mutane kaɗan ne kacal suka san da littattafai ta intanet a lokacin. Dagangan na saki littafi na na farko ta internet."

A matsayinsa na marubucin littafi da wasanni, cikin jerin abubuwan da Alex ya rubuta sun haɗa da littattafai 15 na zube, waɗanda akasarinsu an wallafa su a harsuna uku na Kenya, aka kuma fassara su zuwa Larabci da Sinanci da harshen Czech da Faransanci da harshen Japan da Sweden.

TRT Afrika