Maria Branyas Morera, matar da ta fi tsufa a duniya, ta yi bikin cika shekaru 117 da haihuwa a yankin Catalonia na kasar Spain.
“Tsufa wani nau'in ibada ne. "Ka rasa jin ka, amma a lokacin ne ma kake ji sosai saboda kuna jin yadda rayuwa ke kasancewara, ba hayaniya ba… Sanin cewa za ka mutu na sa ka sake gane muhimmancin rayuwa," ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, tana ambato wata magana da babban malamin ɗariƙar Katolika Pedro Casaldaliga. .
Kundin bajinta na Guinness Book of World Records ya ayyana ta a matsayin wadda ta fi kowa tsufa a duniya a watan Janairun 2023, bayan da ɗaya matar da ta fi kowa tsufa ƴar Faransa Lucile Randon ta mutu tana da shekara 118.
An haife ta a San Francisco a cikin 1907 a zuri'ar Catalan, ta koma zama tare da danginta a Spain lokacin tana da shekaru takwas. A lokacin tafiyar ta Atlantika, ta zama kurma a kunne ɗaya kuma mahaifinta ya mutu saboda tarin fuka.
A cewar Guinness, ta shafe shekaru 23 tana zama a gidan jinya kuma tana cikin koshin lafiya.
Baya ga matsalar ji da rashin ƙarfin jikiotsi, Guinness ta ce tsohuwar ba ta da wasu matsalolin lafiyar jiki ko na hankali kuma tana fuskantar gwajin kimiyya daga masu binciken da ke fatan samun haske kan tsawon rai.
Baya ga "sa'a da kyawawan ƙwayoyin halitta," Branyas ta danganta tsawon rayuwarta zuwa "tsari da kwanciyar hankali da kyakkyawar alaƙa da dangi da abokai da kwanciyar hankali da rashin damuwa da rashin nadama da kuma nisantar mutane masu mugun hali.”
Ta siffanta kanta a shafinta na X da cewa: "Na tsufa, na tsufa sosai, amma ni ba wawiya ba ce."
Ta kuma wallafa a ranar 5 ga Fabrairu cewa yayin da kanta ke ci gaba da tsufa, jikinta yana sakewa. "Ba zan ƙara lokaci mai tsawo," in ji ta.
Amma kuma takan hau shafukan sada zumunta ta wallafa wasu abubuwa kamar sanar da haihuwar da karyar da take kiwo ta yi, kuma tana ba da shawarwarin falsafa.
Kundin Guiness ya ce a yanzu Branyas ce mutum ta 12 mafi tsufa da aka taɓa samu a tarihi, amma idan har ta kai baɗi to za ta koma ta biyar.
Matar da ta fi kowa tsufa da aka taba ajiye tarihinta ita ce ‘yar Faransa Jeanne Calment, wacce ta rayu har zuwa shekaru 122 da kwana 164.