Lambar yabo ta AMVA,  biki mafi girma da ake karrama fina-finai da jarumai da suka yi rawar gani a Afirka

Daga Charles Mgbolu

Masu shirya taron ba da lambar yabo ta Africa Magic Viewers Choice Awards (AMVCA), biki mafi girma da ake karrama fina-finai da jarumai wadanda suka yi rawar gani a Afirka, sun yi kira ga masu hada shirye-shirye a fadin nahiyar kan su gabatar da shirinsu gabannin soma shirin gudanar da taron karo na goma wanda za a yi a cikin watan Mayu.

Sai dai a wannan shekarar tsarin ba da kyautar zai zo da sauye-sauye masu yawa.

"Yayin da muke shirin gudanar bikin cika shekaru goma ... muna kokarin bin wasu muhimman hanyoyi don sake kimanta rukunan lambobin yabo da muke bayar wa tare da daidaita su da zamanin da ake ciki a duniya," a cewar wani sakon bidiyo da shugaban shirye-shirye da tasoshi na MultiChoice a yammacin Afirka, Busola Tejumola ya fitar a ranar Litinin.

"Hakan ya hada da sauke wasu rukunai tare da daidaita wasu da kuma sake yin duba kan yanayin yadda aka zabi wasu tare da kasafta su," in ji ta.

A cewar Tejumola, lambobin yabo na kwazon jarumai sun bi matakai na '' daidaita su sannan za su kasance a karkashin rukunin fitaccen jarumi ko jaruma a matsayin jagora ko wanda za a tallafa a cikin shiri, inda alkalai za su zabi wanda ya yi nasarar lashe kyautar sabanin tsarin kada kuri'a na masu sauraro da aka saba yi a baya.

Za 'a gudanar da taron bikin ba da lambar yabo ta AMVCA karo na goma a cikin watan Mayu 2024 . 

Masu sukar taron bikin na bara sun yi marhabin da labarin sauye-sauye a wannan karon.

Suka

A bara, bikin taron karrama jarumai na AMVCA ya sha suka sosai a shafukan sada zumunta bayan an sanar da sunanyen wadanda suka yi nasara a wasu rukunai.

Masu sukar sun ce, bai kamata a ba da lambar yabo ta fitaccen jarumi ko jaruma daga kuri'un da al'umma suka jefa ba, la'akari da cewa jarumai da suka fi yawan mabiya a shafukan sada zumunta su suka lashe kyautar ba wadanda suka fi kokari a baiwarsu ta wasan kwaikwayo ba.

Haka kuma an yi ta cece-kuce a lokacin da aka cire sunan fitaccen jarumin fina-finan Nijeriya Kunle Remi a cikin jerin sunayen wadanda aka zabo domin karramawa duk da irin rawar da ya taka a fitaccen shirin jarumin shirya fina-finan kasar Kunle Afolayan mai suna Anikulapo, wanda ya aka zabe sau 16 a matakan ba da lambobin yabo.

An yi ta cece-kuce a lokacin da aka cire sunan fitaccen jarumin fina-finan Nijeriya Kunle Remi a cikin jerin sunayen wadanda aka zabo domin karramawa

Ko da yake Kunle ya bayyana cewa cire sunansa da aka yi bai yi wani tasiri a kansa da salonsa da shahararsa ko kuma kuzarinsa.

Kimar Lambar Yabon

''Ba shiri na ba ne, kuma ba za mu samu amsoshi ba, amma na yi farin ciki da duniya ta yi magana a kai... Bai ya rage min kima ta ba. ban jajirce a kan aiki na ba saboda na samu lambar yabo, amma saboda kalubalen da ke ciki, ''kamar yadda Kunle Remi ya shaida wa kafafen yada labarai na cikin gida a kasar.

Shirin AMVCA bai mayar da martani ga wannan sukar ba, amma sabbin sauye-sauye da aka yi sun nuna manufar kiyaye mutunci da kimar lambobin yabon.

"Shirin AMVCA zai ci gaba da jajircewa wajen gudanar da bikin karrama hazaka a masana'antar fina-finai da talabijin ta Afirka." in ji sakon bidiyo naTejumola.

Kawo yanzu dai ba a bayyana sunayen mambobin kwamitin da za su yanke hukunci a kan wadannan rukunoni ba, sai dai AMVCA ya ce alkalan sun kunshi gogaggun masu shirya fina-finai ne daga sassan nahiyar Afirka, kuma shugaban alkalan ne zai tantance wadanda suka yi nasara a rukunai 16 da ba za a kada musu kuri'u ba.

TRT Afrika