Ƴan ƙabilar Kanuri daga kasashe da dama sun hallara a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya, domin bikin raya al'adunsu da aka gudanar a ƙarshen makon jiya.
Ba a taɓa gudanar da irin wannan taro ba. "Abin farin ciki ne la'akari da cewa wannan shi ne taron al'adun Kanuri na farko a yankin Tafkin Chadi," kamar yadda Abdulazeez Mala, jami'in gudanarwa na Ƙungiyar Voices of Lake Chad, wanda ya halarci taron, ya shaida wa TRT Afrika.
“Dukka al'ummar Masarautar Kanem-Borno da aka rusa sun halarci taron baje kolin al’adunsu tare da inganta haɗin kan iyakokinsu da kuma farfaɗo da tattalin arziki da cuɗanya tsakanin mutanen yankin masu ra’ayi ɗaya,” in ji Mala.
Al'ummar Kanuri sun fi zama a yankunan tsohuwar ɗaular Kanem-Borno wacce a yanzu ta mamaye wasu sassan Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, Daula ce mai ƙarfin gaske a yankin a shekarun baya da suka wuce.
Duk da cewa an rusa daular Kanem-Borno a lokacin mulkin mallaka da Ƙasashen Yamma suka yi, yan ƙabilar Kanuri sun ci gaba da alkinta al'adu da harshensu da kuma haɗin kai a tsakaninsu.
“Har ya zuwa wannan lokaci al’ummar Kanuri sun rabu don samun damarmaki a siyasance,” in ji Abdulazeez.
An gudanar da taron al'adun gargajiya ta ƙabilar Kanuri ne a ƙarƙashin jagorancin Shehun Borno da Abubakar Umar Garbai El-Kanemi, wanda shi ne Shugaban Masarautar Borno na yanzu.
Harshen Kanuri ya kasance babban harshe da ake amfani da shi ya zuwa yanzu a yankin kudu maso gabashin Nijar da arewa maso gabashin Nijeriya da arewacin Kamaru.
Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta kafa gidan tarihi na bincike da yawon bude ido da kuma adana kayayyakin tarihi na Kanem-Borno mai dadadden tarihi.