Mutane na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta a Nijeriya kan sabon taken ƙasar wanda Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a ranar Laraba.
Ga dai jerin wasu saƙonni da wasu fitattun mutane a shafukan sada zumunta a ƙasar suka wallafa don bayyana ra'ayoyinsu a kan dokar.
Joeboy (mawaƙi/mai rubuta waƙa)
"A ce duk cikin matsalolin da muke da su a Nijeriya ba abin da za a mayar da hankali a kai sai sauya taken ƙasar? To ai shi kenan."
Adekunle Gold (mawaƙi/mai rubuta waƙa)
A ra'ayina, dama kawai Shugaban Ƙasa biyan Adekunle Gold ya yi ya mayar da sabuwar waƙarsa ta 'Rodo' ta zama taken ƙasar tamu. Mun ga abin da ya ishe mu."
Teni (mawaƙi/mai rubuta waƙa)
"Zan yi kewar Arise o compatriots, na gode da tuna min da ƙuruciyata soai. Sai mun sake haɗuwa, ina son ki."
Kate Henshaw ('yar fim)
"Ana tsaka da wannan tsananin wahalar da gazawar gwamnati a kowane mataki shi ne babu abin da za a yi sai komawa taken Nijeriya da Turawan mulkin mallaka suka ƙirƙiro mana a matsyain wani abu da zai farfaɗo da kishin ƙasa a zuƙatanmu."
5. Chinedu Ekedieze, AKA Aki (ɗan fim/mai barkwanci)
"Ko za mu iya ƙara wasu launukan a kan kore da fari na alamar ƙasarmu?"
Charly Boy (mawaƙi/mai fafutuka)
"Rashin sanin abin da ya dace a yi da rashin ƙwarewa da haɗama da uwa-uba CIN HANCI duka farfagandar ƙarya ba za ta taɓa rufe su ba. Mutanena, abin da yake damunmu ya fi ƙrfin ƙsar nan, YUNWA CE KO TAKEN ƘASA?"
I Go Save (Mai barkwanci)
Ya ce, "To tun da dai za a iya dawo mana da tsohon taken ƙsar nan, ko za ku iya dawo mana da tsohon farashin solar da farashin fetur da tsohon tsarin haraji da tsohon tsarin sufurin jiragen sama da tsohon tsarin tsaro da dai sauran su?"
Pere (ɗan jarida)
"Mene ne dalilin wannan abu? Kuma waye ma ya rubuta tsohon taken ƙasar ne?"
Brymo (mawaƙi/mai rubuta waƙa)
"Shugaba Bola Ahmed Tinubu a hukumance shi ne gwanina da ya fi kowa wato G.O.A.T a cikin duka waɗanda suka shugabanci Nijeriya! Karanta kalaman sabon taken ƙasar.
Siɗirar farkon ce kawai muke buƙata; tana nuna Nijeriya ce ƙasar uwarmu ta gado a yanzu kuma Afirka ne yankin babanmu na gado da ke nuna alamar gidan aure mai mata da yawa don haka za mu iya mayar da hankali kan iyali 'yan gida ɗaya.
Siɗirar da na fi so ita ce 'In brotherhood, we stand,' wato "Mu 'yan'uwan juna ne. Ma'ana dukkanmu iyalan ƙungiya ɗaya ce mai ƙarfi a duniya.
A yanzu Nijeriya ce kawai yankin da ya haɗa 'yan'uwantaka inda kowane yaro da yarinya za su haɗu ƙarƙashin gida ɗaya a ƙasar nan. Ina matuƙar farin ciki.