Fitacciyar mawakiya a Nijeriya Onyeka Onwenu ta rasu tana da shekaru 72: Shafin Facebook 

A ranar Labara ne al’ummar Nijeriya suka tashi da labarin mutuwar fitacciyar mawakiya Onyeka Onwenu wacce ta mutu a asibitin Reddington da ke jihar Legas, a cewar kafofin yada labarai a ƙasar.

Mawaƙiya Onyeka Onwenu ta rasu tana da shekaru 72 a duniya.

Onwenu ta kasance 'yar wasan kwaikwayo kana 'yar jarida sannan 'yar siyasa inda mafi yawan wakoƙinta kan tabo al'amuran da suka shafi zamantakewa da siyasa.

Rahotonni sun yi nuni da cewa mawaƙiyar ta rasu ne a ranar Talata da daddare, bayan da ta yanke jiki ta faɗi a wajen wani bikin murnar zagayowar shekarar haihuwa wata da aka gudanar a birnin Legas.

''An gaggauta kai ta asibitin Reddington, a can ne ta cika,'' kamar yadda kafofin yada labarai a Nijeriya suka rawaito.

'Yan Nijeriya na ta jimamin mutuwar mawaƙiyar a kafofin intanet, a yayin da suke ta yaɗa wani bidiyo da take rera ɗaya daga cikin waƙoƙinta mai taken ‘'One Love'' a wurin bikin jim kadan kafin rai ya yi halinsa.

A cikin bidiyon, an ga Onwenu tana taka rawa cikin nishaɗi da annashuwa tare da shagaltar da mahalarta taron waɗanda suka yi mata bankwana na ƙarshe.

A sakon ta'aziyarsa ga 'yan'uwa da iyalan marigayiyar, shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa “za mu ci gaba da rayuwa da Mis Onwenu a cikin waƙoƙinta'' in ji sanarwar da shugaban ya fitar ranar Laraba ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan kafofin yada labarai, Ajuri Ngelale.

''Shugaban ya yi tuni tare da jinjina ayyukan fasaha da nishaɗi da dama waɗanda marigayiyar ta yi wajen inganta rayuwar jama'a da kuma wata waƙarta ta haɗin gwiwa da fitaccen mawaƙin ƙasar King Sunny Ade mai taken 'Wait for Me'' wadda ta mayar da hankali kan gangamin tsarin iyali a shekarun 1980.''

An haifi mawaƙiyar wadda ta kwashe tsawon shakaru 40 a fagen nishaɗi a ranar 31 ga watan Mayun 1952.

TRT Afrika