Shahararrun masu shirya fina-finai da gwarazan ‘yan fim na ta samun karramawa daga kasashe tun bayan da aka shiga kakar karrama ‘yan fina-finai a 2023.
Irin wannan bikin na baya-bayan nan ya zo ne a farkon makon nan inda ya zamo abin tattaunawa a sashen nishadi na labarai.
Toyin Elebe, wanda wani dan Nijeriya ne mai shirya fim, ya samu kyauta a bangaren wanda ya fi kwarewa wurin dora murya a bikin Cannes World Film Festival kan shirin documentary na Vote true.
Tuni dama shirin na Vote True ya samu kyauta a gasar da aka yi a New York kuma aka zabe shi a daya daga cikin fina-finan da za a karrama a Bikin Fina-Finai na Kasa da Kasa a Sweden da Lisbon.
Shekarar masu shirya fina-finai na Afirka
Fina-finan Afirka ta Kudu irin su Ninja Moon Showdown da The Omen da Extravagant Ways To Say Goodbye da The Last Days of Elizabeth Costello da Riel da Moments of Dying duk an karrama su a bikin bana.
Fim din Insha'Allah a boy na mai shirya fina-finai na Masar Amjad Al-Rasheed ya samu kyauta a gasar Gan Foundation da kuma gasar Rail d’Or.
Shirin gasar AFFRIF
A dayen bangaren kuwa, masu shirya gasar fina-finai ta Afirka wato Africa International Film Festival sun shirya wa karo na 12 na gasar wadda za a yi tsakanin 5 zuwa 11 ga watan Nuwambar 2023.
Wadanda suka shirya gasar sun sanar da cewa fim din nan na Orah wanda mai shirya fim din nan na Nijeriya da Canada, da shi ne ake sa ran bude gasar.
AFRIFF wani shiri ne na fina-finai na kasa da kasa wanda ke shiga cikin duniyar shirya fina-finai, inda ake halartarsa daga ko ina cikin Afirka da sauran kasashen waje.
Wadanda suka shirya gasar sun ce dama ce domin musayar bayanai da shawarwari da kuma kulla abota ta kasuwanci da za ta sa a amfana.
Babban abu da za a yi a lokacin gasar shi ne gabatar da kyaututtuka, bayan masana da alkalai sun tantance wadanda za a ba.