Mawakiyar Nijeriya Tiwa Savage ta ce sabon fim ɗin da ta shirya, 'Water and Garri' na samun karbuwa sosai a kasashe 14 na Afirka da wajen nahiyar.
Tiwa, wadda cikakken sunanta shi ne Tiwatope Omolara Savage, ta fitar da sakon yin murna a shafin X don murnar nasarar shoirin fim din ta, wanda ake kallo a manhajar Prime Video.
"Yana kan gaba a kasashe 14. Gidiya ga ahalin WAG (Water And Garri) a duk fadin duniya bisakauna da goyon bayan da suka nuna," in ji Savage a sakon nata.
Shirin fim din Water And Garri da Savage ta shirya tare da mai shirya fina-finai a Nijeriya Jimi Adesanya, ya fara fita ta manhajar Prime Video a ranar Juma'a, 10 ga Mayu, 2024.
A fadin Tiwa Savage "Water And Garri na ta samun karbuwar masu kallo a Nijeriya, Ghana, Kamaru, Benin, Rwanda, Togo, Zmabia, Cyprus, Uganda, Ukraine, Tanzania, Qatar da Afirka ta Kudu.
Shirin fim din na bayar da labarin Aisha (Savage da kanta ce ta fito a matsayin ta), mai sana'ar dinki da ke da burin dawo wa kauyensu bayan shafe tsawon shekaru a Amurka. Ammma bayan zuwan ta sai Aisha ta gano cewar wajen da a baya take kira gida a yanzu cike yake da rikici da tashin hankali.
An dauki shirin fim din da Meji Alabi ya bayar da umarni a Cape Coast, Ghana, kuma ya kunshi jarumai irin su Mike Afolarin, Andrew Bunting da Jemima Osunde.