Yadda ake faretin Diturupa a Afirka ta Kudu. / Hoto: AA

Yadda ake ganin dakaru suna fareti ta cikin kauyuka ana buga musu ganga, ya sake dawowa a arewa maso yammacin Afirka ta Kudu wanda biki ne na al’ada da ya samo asali tun daga yakin duniya na farko.

A duk shekara a ranar 26 ga watan Disamba, rukuni daban-daban sanye da kayan sojoji na gudanar da bikin Diturupa a kauyen Makapanstad – wanda wata al’ada ce da aka shafe shekara 100 ana yin ta.

Diturupa, wadda ke nufin dakaru su saka kayan sarki, a harshen Setswana, bikin yana tunawa da yadda sojojin Afirka suka bayar da gudunmawa a yake-yake daban-daban.

Sojojin da suka dawo daga yakin duniya na biyu sun nuna irin kwarewar da suka samu ta hanyar koya wa mutanen kasar yadda ake fareti da kayan soji da yanayin saka kayan.

Yadda masu faretin ke nishadantarwa a lokacin da suke wake-wake

Sojojin sun hada atisayen da aka koya a lokacin yakin - musamman daga sojojin Scotland - tare da al'adun gida.

An saba gabatar da faretin a gaban shugabannin gargajiya da mazauna garin a duk shekara.

Bikin Diturupa ya sake habaka inda tuni ya zama wani biki na al’ada. Mahalarta taron na saka kayan sojoji tare da kaya masu zayyana irin ta Afirka domin bayar da launi mai kyau.

Ana karfafa musu gwiwa su rinka rawa da waka. Ana bayar da maki na faretin dangane da kayayyakin sakawa da rawa da waka fareti wanda a karshe ake bayar da kyaututtuka.

Diturupa

Ana karfafa gwiwar matasa kan su mayar da hankali wurin bikin wanda aka bayyana cewa taimaka wa yawon bude ido a yankin.

TRT Afrika