Diamond Platnumz ya fitar da kundin wakoki guda 11 a rayuwarsa. Hoto: Diamond Platnumz      

Ba a banza ba ake ta maganar fitaccen mawakin Tanzania, Diamond Platnumz a kafofin sadarwa.

Ana taya mawakin, wanda asalin sunansa Naseeb Abdul Juma murna ne bayan an saurari wakokinsa sau sama da sau miliyan 400 a manhajar sauraron wakoki ta Boomplay.

Mawakin ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa salon wakar Tanzania mai suna Bongo Flava, wanda wannan nasarar ce ta sa ya zama zakaran gwajin dafi a harkokin waka a yankin Gabashin Afirka da ma wasu sassa na duniya.

Diamond ya samu nasarar kai wa wannan matakin ne bayan fitattun wakokin da suka yi shuhura da ya fitar ta hanyar hadaka da wasu mawakan na duniya.

Wakarsa ta karshe-karshen nan mai suna Mapoz da ya sanya mawakan Tanzania Mr Blue da Jay Melody a ciki an saurare ta sama da sau miliyan 18 a manhajar Boomplay da kuma sama da miliyan 14 a YouTube.

Diamond ne ya lashe kyautar Gwarzon Mawaka a taron karrama mawaka ta MTV Europe Music Awards na shekarar 2023. Hoto: Others

A shekarar 2023, manhajar sauraron waqa ta Spotify ta ayyana sunan Diamond a cikin zaratan mawaka a cikin rahotonta na karshen shekara, inda ta bayyana shi a cikin zaratan mawakan da aka fi sauraron wakokinsu a yankin Gabashin Afirka baki daya na tsawon lokaci.

Diamond yana cigaba da samun dimbin masoya a yankin Gabashi da Tsakiyar Afirka. Shi ne ya zama mawaki mazaunin yankin Afirka na farko da ya haura makallata biliyan 1 a YouTube.

Babban abin da ya sa Diamond ya yi zarra shi ne yadda yake iya hada nau’ukan kida daban-daban da salon wakoki daban-daban domin fitar da nasa.

A Afrilun 2024, Diamond ya lashe kyautar wanda wakokinsa suka fi tashe na shekarar 2024 a taron karrama masu nishadi na 2024 East Africa Entertainment Awards (EAEA).

A Nuwamban 2023, Diamond ya lashe kyautar Gwarzon Mawakin Afirka na 'Best African Act' a taron karrama mawaka na MTV Europe Music Awards a Faransa.

Fitaccen mawakin na Tanzania wanda yake jan zarensa a yanzu ya doke zaratan mawaka ne irin su Burna Boy da Asake na Nijeriya wajen lashe kyautar mai daraja.

Sauran wadanda ya doke sun hada da dijen Afirka ta Kudu kuma fitaccen furodusan wakoki Tyler ICU da mawakin Kamaru Libianca.

TRT Afrika