Daga Pauline Odhiambo
Zanen Cornelius Annor na kama da wani yanayi da ke tunatar da mutum lokutan baya da suka shuɗe.
Mai haɗe-haɗen salon zanen ya kan samu ƙwarin gwiwar yin ayyukansa ne daga tarihin abubuwan da suka faru a lokacin tasowarsa a Ghana a shekarun 1990.
Ayyukansa sukan tunatar da masu sha'awar zane kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin 'yan uwa da kuma muhimman lokutan da aka kasance tare.
''Na kan samu karfin gwiwar yin zane na ne daga hotunan albam ɗin iyali,'' kamar yadda mai fasahar zanen ɗan asalin Ghana ya shaida wa TRT Afirka.
"Yawancin zanen da nake yi na 'yan uwa na ne waɗanda suke kusa da ni sosai ko kuma mutanen da na zaɓa in kasance tare da su saboda sun zama tamkar dangi a gare ni.''
Salon haɗe-haɗen zane na Mixed media wani nau'in fasahar zane ne da ya haɗa fiye salo ko kayan aiki guda ɗaya, a cewar Cibiyar haɗe-daɗen fasahohi.
Salon zanen na iya zuwa cikin nau'i daban-daban, amma waɗanda aka fi sani guda uku ne, sannan mafi yawa daga cikinsu sun ƙunshi abubuwa daban-daban da ake amfani, kamar fenti da tufafi da takarda da sauran wasu kayayyakin.
Kazalika Annor ya kan samu karfin gwiwar hada zanensa ne daga tarin hotunan mutanen ɗa daga Taskar Intanet, waɗanda suke nuna bambance-bambancen kyawawan tarihin al'adun baƙin fata.
Zanensa mai suna "Yonko S3 Onua,'' ya samo asali ne daga Taskar Intanet kuma fassararsa na nufin ''aboki kamar ɗan'uwa'' a harshen Twi na Ghana.
Zanen ya nuna wasu maza biyu sanye da kayatattun launin tufafin Afirka, dangantakarsu ta bayyana a yanayin jikinsu.
''Tambari kan tufafi da ake gani a yawancin ayyukan da na ke, na kan sa su ne don jawo hankalin masu kallo zuwa zamanin baya, yayin da salon haɗe-haɗen abubuwa na collage kan sanya mutum ya ji yana wannan zamani,'' kamar yadda Annor ya bayyana salon aikin zanensa.
"Na kan haɗa waɗannan dabarun zanen a lokacin aikina,'' in ji mai fasahar zanen wanda ya kammala karatunsa daga kwalejin Fasaha da Zane na Ghanatta.
Zamanin rawar disco
Waƙa ta kan taka muhimmayar rawa a tsarin ƙirƙire-ƙirƙiren Annor.
Yawancin zane-zanensa su kan bayyana wurare masu ƙayatarwa inda ake nuna mutane suna rawa a ƙarkashin fitilar wuta mai haskawa na disco ko kuma a filin shaƙatawa da raye-rayen da mai kallo ne kawai zai iya fahimta.
"A Time With Fela" yana ɗaya daga cikin irin zanen da ya yi, inda masu nishaɗi ke rawa sanye da ɗogayen wandunan 'yan gayu masu faɗi daga ƙasa a shekarun tsakiyar 1960 zuwa 1990.
''Wannan zanen yana daga cikin ayyukana da na yi a shekarar 2023 a taron baje kolin Over Manhattan gallery a birnin New York,'' kamar yadda Annor ya bayyana kan ayyukanshi da ya yi wanda ya mai take da "Fabric of Time and Family."
''Ina sauraren waƙoƙin Fela Kuti da dama a yayin da nake ayyukan zanen da na yi guda 15 a taron baje kolin, shi ya sa na sanya masa suna da 'A Time with Fela’ wato lokaci da Fela,” kamar yadda mai salon haɗe-haɗen zanen mai shekaru 34, wanda yake sayar da ayyukansa a duban farashin daloli a kasuwannin duniya ya bayyana.
Zanen hoton Mahaifinsa
Mahaifin Annor, mai aiki sassaƙa ne kuma ya rasu yana ɗan shekara takwas.
Wasu daga cikin zane-zanen da ya ƙirƙira sun bayyana hotunan mahaifinsa da aka manna a jikin bango don tunawa da mutumin da ya ƙarfafa masa ya zama mai zane.
"Mutumin da aka zana a wannan zanen ƙwararre ne wanda ya kware wajen rubutu shi ma. Shi ne mahaifin ɗaya daga cikin mataimaka na a a wajen aikin," kamar yadda Annor, wanda ayyukansa suka bazu a wuraren baje kollin fasahohi da dama a duniya ya shaida wa TRT Afrika.