By Pauline Odhiambo
Tyla 'yar Afirka ta Kudu, Seun Kuti na Nijeriya, da Amaarae ta Ghana na daga cikin mawakan da za su cashe a wajen bikin Coachella na 2025.
Bikin waƙe-waƙe na Coachella da za a gudanar a Indio, California, ya sanar yadda taron na mako biyu zai kasance, wanda za a yi a tsakanin 11 da 13, da 18 da 20 ga Afrilun 2025.
A ranar Laraba makonni uku a suka gabata ne Goldenvoice suka fitar da sanarwa, wadanda a farkon kowacce shekara suke sanar da lokaci da wajen da zaa gudanar da shirin.
Da yake mayar da martani a shafin X, Tyla da ta zaku ta ce duk da a baya ta samu damarmakin halartar Coachella, ta yi alkawarin a wannan karon ne za ta je taron a matsayin cikakkiyar mawakiya.
Mafarki ya zama gaske
"Na samu damarmaki da dama amma na rantse a karon farko da zan halarci Coachella, zan kuma yi waka... ku kalla yanzu!" in ji mawakiyar mai shekaru 22.
Alile Phogele, malamin kida da waka a Jihannesburg inda wadda ta lashe gasar Grammy ta girma ya fada wa TRT Afirka, cewa "Tyla ce ma'anar tabbatar da mafarki ya zama gaskiya.
Tana aiki tukuru, tana addu'a da kuma nuna hanyarta ta zama zakakurar waka a duniya. Lallat ta hadu sosai."
Coachella biki ne da a kowacce shekara yake sauya saharar California zuwa matattarar mawaka ta duniya.
Seun Kuti na da kambin kasancewar mawakin Nijeriya na farko da ya halarci bikin Coachella tun a 2012. Tun wannan lokacin, mawakan Nijeriya irin su Eazi, Burna Boy (2019), Ckay (2022), da Tems (2024) sun halarta, inda suka daga martabar salon wakokin afrobeat.
Shigar da mawakin Nijeriya Rema cikin wadanda za su cashe a wajen bikin na 2025 ya sanya shi zama mai halarta a karon farko
Benin Boys da aka san,i da wakokinsa na 'Charm' da 'Benin Boys', 'Prince of Afro-rave' na ci gaba da samun mazauni a matakin wake na kasa da kasa.
Sannan wakarsa ta "Calm Down" ta zama ta farko a wakokin afrobeat a tarihi da suka samu sauraro sama da biliyan guda a Amurka, kamar yadda shafin Chart Data da ke sanya idanu kan wakoki ya bayyana.
Ana kafa tarihi
Mawakiyar Gana kuma 'yar Amurka da ke rubuta waka, Ama Serwah Genfi da aka fi sani da Amaarae ta shirya kafa tarihi na zama 'yar kasar Gana ta farko da ke halartar bikin Coachella don cashewa.
Bana shekara ce da ta kawo shuhura ga "Angels in Tibet", wakar da ta rera a wajen Bikin Roskilde a kasar Denmark a watan Yuli.
Amaarae da aka sani sosai da wakokinta na R&B, Afroneats da Alte, ta zama mace 'yar kasar Gana ta farko da ta samu sauraren wakoki biliyan guda a manhajojin sauraren wakoki.
Da yake mayar da martani ga zabin Amaarae don cashewa, mai koroso na kasar Gana, Akosua Frimpong ya fada wa TRT Afirka cewa, "Amaarae na da basirar waka kuma kwararriyar mai rubuta waka ce. Na zaƙu na ga cashewar ta a bikin Coachella mai zuwa."
Tare da mahalarta sama da 125,000, Coachella ya samu wajen zama babban bikin wakoki a duniya, yana kawo kida da waka daga manyan sunaye a fannoni daban-daban.
Daga cikin wadanda za su fito a bikin na watan Afrilun 2025 har da Lady Gaga, Green Day, Post Malone, Travis Scott. Missy Elliot, GloRilla da Megan Thee Stallion