Daga Kudra Maliro
A can cikin gabashin Jumhuriyar Dimukradiyyar Congo, inda kungiyoyi masu dauke da makamai suke addabar al'ummar kauyuka, kuma inda ake da sansanonin soji, wani mai barkwanci dan shekara 23 ya fito da salon fadakarwar zaman lafiya ta hanyar barkwanci.
Gloire Bisimwa yana yin tashe wajen al'ummar Congo da ke kafar TikTok, inda yake yin bidiyoyi da ke kwaikwayar fitaccen dan barkwancin nan na zamanin baya, dan Ingila, Charlie Chaplin, wanda ya rasu tun shekarar 1977.
Dan barkwancin da ake wa lakabi da Cali-calin Congo ya fada wa TRT Afrika cewa, "Tun sanda nake yaro, ina bibiyar fina-finan Charlie Chaplin na barkwanci kuma yana burge ni. Ina son yadda yake nishadantar da mutane".
Ina tuna mahaifiyata tana ce min na fara yin wanki, kafin na zauna kallon fim din Charlie, saboda shirye-shiryensa suna kayatar da ni matuka.
Gabashin Congo ya kasance mai fama da rikici tsawon shekaru sama da 30, kuma yawancin matasan yankin sun shiga harka miyagun kwayoyi saboda tasirin rikicin kan rayuwarsu.
Wasunsu sun kwadaitu da kungiyoyin mayakan sa-kai inda suke shigar da su mummunar harkar.
Sakonnin zaman lafiya
Amma shi Gloire ya zabi bin wata hanyar, ba ta bin miyagun mutane ba. Yana amfani da fikirarsa don yada sakon zaman lafiya ga matasa, inda yake koyar da su kauracewa shiga kungiyoyin 'yan ta'adda.
Gloire yana da dubban masoya a TikTok kuma mutane da yawa a yankin Bukavu suna kallon sa a matsayin 'mai baiwa daga Allah', saboda yana nishadantar da mutane.
Odia Kabulo wani dalibi ne daga garin Bukavu kuma mai amfani da TikTok, ya ce "Na san Gloire 'yan watanni yanzu, ta dalilin bidiyoyin barkwancinsa a TikTok. Yana debe min kewa. Don haka nake ganin sa tamkar wani ruhi mai kawo wa mutane farin ciki".
Gloire ya ce yana kashe daruruwan daloli wajen sayen sutura da kayayyakin da za su sa ya yi kama da Charlie Chaplin.
Dan barkwancin ya ce, "Ina yin odar sutura daga birnin Kinshasa (babban birnin kasar) sannan ina yawan dinka suturar da kaina".
Ya kara da cewa, "Baya ga kafofin sadarwar zamani, ina kuma shirya taron barkwanci a coci, da garuruwa a fadin duniya, don isar da sakonnin zaman lafiya da kawo wa mutane nishadi."
Asalin Charlie Chaplin wani tauraron wasan barkwanci ne da ya samu shuhura a duniya a matsayin dan wasan kwaikwayon da ba a magana, sannan ya fito a matsayin Little Tramp a fina-finansa na shekarun 1914 zuwa 1936.