Sarkin Asante Otumfuo Osei Tutu II yana zama kan karagar zinare, wanda ke nuna haɗin-kai da iko na al'ummar Asante, / Hoto: Mahama/Facebook

Daga Charles Mgbolu

An ji raujin ganguna a fadar sarauta ta Manhyia da ke Kumasi, Ghana, yayin da ɗaruruwan mutane suka taru ranar Lahadi, 19 ga Janairu, don halartar bikin al'adu mai suna Akwasidae Kese na 2025.

Bikin Akwasidae Kese muhimmin biki ne na al'ummar Asante, wata babbar ƙabila a ƙasar Ghana da ke Yammacin Afirka. Al'ummar Asante tana cikin dangin al'ummar ƙabilar Akan, wadda ita ta haɗa da sauran ƙabilu kamar Fante, da Akuapem, da Akyem.

Bikin na ranar Lahadi shi ne na farko a farkon shekara a jerin bukukuwan al'ummar Asante, kuma babban jigo ne na tabbatar da tasirin Asantehene da na masarautar Asante.

Shugaban ƙasa John Mahama ya gode wa Asantehene kan jagorancin wannan biki. / Hoto: Mahama/Facebook

Bikin wani babban biki ne na ƙabilar Asante wanda ke gayyato mutane daga duk faɗin Ghana da ma ƙasashen duniya.

Sabon shugaban Ghana John Mahama, ya halarci taron don gimama sarkin Asantehene, Otumfuo Osei Tutu II.

A wajen taron, Shugaba Mahama ya ce, “Gina tituna, da kasuwanni, da asibitoci, da faɗaɗa samar da lantarki da ruwan sha zuwa gidaje, ayyuka ne da sarkin ke bayar da shwarar aiwatarwa.”

Fadar da ke Dwabrem takan ci ado, da kaloli da kaɗe-kaɗe. mahalarta suna shiga da ƙyallen Kente wanda na saƙi ne, da aka sani da ƙabilar Asante — da sauran tufafin gargajiya da ke da ƙayatarwa.

Akan shirya bikin da ya ƙunshi salo-salo, wanda ake fara wa da zuwan sarki Asantehene, wanda ake ɗauko shi a kan karaga, wadda ake wa ado ana yi masa kiɗa ana busa ƙaho.

Bikin yana nuna sabuwar shekara a kalandar al'adar Asante. / Hoto: Mahama/Facebook

Ayarin yana nuna nau'in al'adun sarauta, inda mahalartan ke ɗaukar takubba, lemomi, da sauran kayayyakin gargajiyar Asante.

Sarkin Asantehene zai zauna a kan karagar zinare, wadda ke nuna haɗin-kai da ikon ƙabilar. Ana kallon sa a matsayin wakilin ruhin ƙasar Asante kuma ba a bari ya taɓa ƙasa.

Bikin ya ƙunshi tarin al'adu kamar watsa mai ga kakannin ƙabilar, da raba abinci da abin sha da raye-raye na gargajiya.

TRT Afrika