Daya daga cikin sabbin zanen Tomiwa shi ne 'Goddess' - hoton da ya dace da wata budurwa 'yar Afirka sanye da wani salon aski na Afirka na musamman. Photo: Tomiwa

Daga Pauline Odhiambo

Abubuwa uku sun fito fili a cikin fasahar Tomiwa Arobieke - ƙwaƙƙwaran salon gyaran gashi na Afirka da kyawawan yanayin furanni da launin ruwan ƙasa mai zurfi.

Mai fasahar zanen na Nijeriya ya sami ƙwarin gwiwa daga al'adunsa na Yarbawa da kuma al'adun Afirka daban-daban waɗanda ke baje kolin kyawawan salo na asali.

"Ina son nuna salon rayuwa na musamman na Afirka a cikin zane-zanena da ke bayyana irin tufafinmu da salon aski daban-daban," kamar yadda mai zane-zanen ya shaida wa TRT Afrika.

A cewar dandali na Clarendon Fine Art, nau'in ya haɗa da hotuna masu nuna abubuwa da al'amura da kuma hotuna.

Zanen matan da ya fi yi a kusan dukkan ayyukansa na fayyace salon gyara gashi. Photo: Tomiwa

Bayyana al'adu

Daya daga cikin sabbin zanen Tomiwa shi ne 'Goddess' - hoton da ya dace da wata budurwa 'yar Afirka sanye da wani salon aski na Afirka na musamman.

Kallonta mai cike da ƙwarin gwiwa da nutsuwa ya yi daidai da sanyin launin rigarta. "Na fi so in yi wa mata zane-zane saboda suna fitar da kyawawan al'adun Afirka," in ji mai zanen mai shekaru 25.

Zanen matan da ya fi yi a kusan dukkan ayyukansa na fayyace salon gyara gashi - waɗanda aka saƙa don kwaikwayon ainihin yadda abin yake.

Hotunan zanensa mai taken 'Elegance,' 'Sarauniyar Afirka' da wasu da yawa suna nuna salon gyara gashi da sauran abubuwa na musamman na Afirka.

Shawararsa ga masu zane da ke tasowa ita ce: "Zane abu ne da ke buƙatar haƙuri, don haka ku ci gaba da yi. A hankali za ku yi zarra.". Photo: Tomiwa

Karfin zanen hotunan ma'aurata

"Ina kuma jin daɗin yin zanen hotunan ma'aurata saboda na ga manufar soyayya a yanayin Afirka yana da ban sha'awa," in ji ɗan asalin jihar Ondon.

Ayyukan zanensa mai suna ‘Companion’ wanda aka zana a cikin 2022 na ɗaya daga cikin aikinsa na farko da ke nuna ma'aurata.

Ya zana hotuna masu kama da juna da yawa tun na farkon, inda yake ƙara abubuwa da suka shafi labaran inganta lafiya da haihuwa da yalwa.

"Bayyana soyayya tsakanin ma'aurata kuma yana inganta zaman lafiya tare da wasu yanayi kuma yana inganta haɗin kai," in ji Tomiwa.

Photo: Tomiwa

‘Aro Meta’

Wani aikin na Tomiwa mai taken ‘Aro Meta’ ya kara yin bayani kan dankon zumunci.

“A yaren Yarbanci ‘Aro meta’ kalma ce ta abokai da suke da kusanci da dabi’arsu,” in ji shi.

Sannan kuma Tomiwa kan yi zane a kan 'ɗabi'un maza' don nuna ƙarfin dangantaka da abota da sauran mu'amala da tke tsakanin maza.

Photo: Tomiwa

Damarmaki

Tomiwa ya yi zanuka da dama da ke fayyace zamantakewa. An sha nuna zane-zanensa a wurare daban-daban a faɗin duniya.

Ya danganta nasararsa da tsayawa ƙyam a kan abin da yake sha'awa da kuma zaɓar zane a matsayin aikinsa duk da ƙalubalen da ke tattare da hakan.

Matashin wanda ya koyi zane a karan-kansa ya yi karatunsa ne a makarantar Polytechnic a Ibadan inda ya yi difloma a fannin kimiyya da fasaha.

"Na fara ne da zane-zane da fensir inda har daga baya nake yi wa mutane suna biyana," in ji matashin mai zanen.

Photo: Tomiwa

Mayar da hankali kan zane

Bayan ya kammala sai ya yi aiki na ɗan gajeren lokaci a wani banki kafin daga bisani ya mayar da hankalinsa kacokan kan zane.

"Daga wannan aikin ne na samu damar adana wasu 'yan kuɗaɗe don sayen kayayyakin yin zane," ya ce. "Amma na daɗe kafin na fara sayar da zanena."

A yanzu ana sayen zanukan Tomiwa tun ma kafin ya kammala zana su.

Aikinsa na baya-bayan nan shi ne na 'Goddess' wanda aka saya tun kafin ya kammala.

Shawararsa ga masu zane da ke tasowa ita ce: "Zane abu ne da ke buƙatar haƙuri, don haka ku ci gaba da yi. A hankali za ku yi zarra."

TRT Afrika